Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 21

Yahaya 21:3-11

Help us?
Click on verse(s) to share them!
3Saminu Bitrus yace masu, “Zani su.” sukace masa “Mu ma za mu je tare da kai.” Sai suka fita suka shiga jirgi, amma a daren nan basu kama komai ba.
4To, gari na wayewa, sai ga Yesu tsaye a bakin gaci, amma almajiran basu gane cewa Yesu bane.
5Sai Yesu yace masu, “Samari, kuna da wani abinda za a ci?” Suka amsa masa sukace “A'a”.
6Yace masu, “Ku jefa taru dama da jirgin zaku samu wasu.” Suka jefa tarunsu har suka kasa jawo shi don yawan kifin.
7Sai almajirin nan da Yesu yake kauna yace wa Bitrus, “Ubangiji ne fa!” Da Saminu Bitrus yaji, Ashe, Ubangiji ne, yayi damara da taguwarsa, (don a tube yake), ya fada a tekun.
8Sauran almajiran kuwa suka zo a cikin karamin jirgi, (domin basu da nisa da kasa, kamar kamu dari biyu zuwa sama), janye da tarun cike da kifi.
9Da isowarsu gaci, sai suka ga garwashin wuta a wurin da kifi akai, da kuma gurasa.
10Yesu ya ce masu “Ku kawo wandansu daga cikin kifin da kuka kama yanzu”.
11Sai Saminu Bitrus ya hau, ya jawo tarun gaci, cike da manyan kifaye dari da hamsin da uku (153). Amma duk da yawansu, tarun bai tsage ba.

Read Yahaya 21Yahaya 21
Compare Yahaya 21:3-11Yahaya 21:3-11