Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 19

Yahaya 19:35-40

Help us?
Click on verse(s) to share them!
35Wanda ya ga wannan, shi ya zama shaida, shaidarsa kuwa gaskiya ce. Ya sani cewa abinda ya fada gaskiya ne saboda ku ma ku gaskata.
36Wadannan sun faru ne domin a cika nassi, “Babu ko daya daga cikin kasusuwansa da za'a karya”.
37Kuma wani nassin yace, “Zasu dube shi wanda suka soka.”
38Bayan wadannan abubuwa, Yusufu mutumin Arimatiya, wanda yake almajirin Yesu ne (amma a boye saboda tsoron Yahudawa) ya roki Bilatus izini domin ya dauke jikin Yesu. Bilatus kuwa ya bashi izini, sai Yusufu yazo ya dauki jikin.
39Nikodimu ma ya zo, wanda da farko ya zo wurin Yesu da daddare, ya kawo hadin man kamshi na mur da al'ul wajen nauyin awo dari.
40Sai suka dauki jikin Yesu suka sa shi a likkafanin lillin tare da kayan kamshin nan, domin jana'iza bisa ga al'adar Yahudawa.

Read Yahaya 19Yahaya 19
Compare Yahaya 19:35-40Yahaya 19:35-40