Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Romawa - Romawa 1

Romawa 1:3-12

Help us?
Click on verse(s) to share them!
3Game da Dansa ne, haifaffe daga zuriyar Dauda ga zancen jiki.
4Ta wurin tashinsa daga mattatu aka aiyana shi ya zama Dan Allah ta wurin ikon Ruhu na tsarkakewa. Yesu Almasihu Ubangijimu.
5Ta wurinsa muka karbi alheri da manzanci sabo da biyayyar imani a cikin dukkan al'ummai, domin darajar sunansa.
6cikin wadannan al'ummai kwa, ku ma an kiraku ku zama na Yesu Almasihu.
7Wannan wasika ga dukkanku ne da kuke cikin Roma, kaunatattu na Allah, kirayayyun mutane tsarkakakku. Bari alheri ya kasance tare daku, da salama daga Allah Ubanmu, da kuma Ubangiji Yesu Almasihu.
8Abu na farko dai ina yi wa Allah na godiya ta wurin Yesu Almasihu domin ku duka, domin kuwa ana labarta bangaskiyarku ko ina a cikin dukkan duniya.
9Domin kuwa Allah shi ne shaida ta, wanda nake bautawa a cikin ruhuna a cikin bisharar Dansa, yadda a koyaushe na ke ambaton ku.
10A kullum ina roko cikin addu'o'ina domin ta kowanne hali in yi nasarar zuwa gare ku da izinin Allah.
11Gama ina marmarin ganin ku, domin in baku wata baiwa ta ruhaniya, domin in karfafa ku.
12Wato ina dokin in sami cikakkiyar karfafawa a cikin ku, ta wurin bangaskiyar junanmu, wato tawa da taku.

Read Romawa 1Romawa 1
Compare Romawa 1:3-12Romawa 1:3-12