Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Romawa - Romawa 13

Romawa 13:6-10

Help us?
Click on verse(s) to share them!
6Saboda wannan ne kuke biyan haraji. Don masu mulki bayin Allah ne, wadanda suke yin haka kullum.
7Ku bawa kowa hakkinsa; haraji ga mai haraji; kudin fito ga mai fito; tsoro ga wanda ya cancanci tsoro; girma ga wanda cancanci girmamawa.
8Kada ku rike bashin kowa, sai dai ku kaunaci juna. Domin duk wanda ya kaunaci dan'uwansa ya cika doka.
9To, “Kada kuyi zina, kada kuyi kisa, kada kuyi sata, kada kuyi kyashi, idan har akwai wata doka kuma, an takaita ta a wannan jimlar: “Ka kaunaci dan'uwanka kamar kanka.”
10Kauna bata cutar da makwabci. Domin haka, kauna tace cikar shari'a.

Read Romawa 13Romawa 13
Compare Romawa 13:6-10Romawa 13:6-10