Text copied!
Bibles in Hausa

Romawa 13:6-10 in Hausa

Help us?

Romawa 13:6-10 in Litafi Mai-tsarki

6 Saboda wannan ne kuke biyan haraji. Don masu mulki bayin Allah ne, wadanda suke yin haka kullum.
7 Ku bawa kowa hakkinsa; haraji ga mai haraji; kudin fito ga mai fito; tsoro ga wanda ya cancanci tsoro; girma ga wanda cancanci girmamawa.
8 Kada ku rike bashin kowa, sai dai ku kaunaci juna. Domin duk wanda ya kaunaci dan'uwansa ya cika doka.
9 To, “Kada kuyi zina, kada kuyi kisa, kada kuyi sata, kada kuyi kyashi, idan har akwai wata doka kuma, an takaita ta a wannan jimlar: “Ka kaunaci dan'uwanka kamar kanka.”
10 Kauna bata cutar da makwabci. Domin haka, kauna tace cikar shari'a.
Romawa 13 in Litafi Mai-tsarki