Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Markus - Markus 7

Markus 7:26-36

Help us?
Click on verse(s) to share them!
26Matar yar kasar Girka ce, kuma asalinta daga Fonishiya take. Ta roke shi da ya fitar da mugun ruhun nan daga diyarta.
27Sai ya ce mata, “Bari a ciyar da 'ya'ya tukuna. Domin bai kamata a dauki abincin yaya a ba karnuka ba”.
28Sai ta amsa masa cewa, “I, Ubangiji, Karnukan ma sukan ci abincin da ke fadowa daga teburin 'ya'yan.”
29Ya ce mata, “domin kin fadi haka, kina iya ki tafi domin aljani ya fita daga diyarki.”
30Ta koma gida sai ta iske diyarta na kwance akan gado, aljanin ya fice daga jikinta.
31Ya sake fita daga shiyar Sur, ya biyo ta Sidon, har zuwa tekun Galili a shiyar Dikafolis.
32Sun kawo masa wani kurma, kuma bebe ne shi, suna rokansa ya dora hanuwansa a bisansa.
33Sai ya jawo shi daga taron jama'ar, zuwa gefe, sai ya sa hanunsa a kunuwan beben bayan ya tufa yawunsa, sannan ya taba harshensa.
34Ya dubi sama, ya ja numfashi ya ce masa, “Ifatha”, wato, “bude!”
35Nan da nan ya mayar masa da jinsa. abinda ya daure harshensa ya sake shi, sai ya fara magana da kyau.
36Ya umarce su da kada su gaya wa wani. Amma duk da umarnin da yake basu, suna ta shaida shi ko'ina.

Read Markus 7Markus 7
Compare Markus 7:26-36Markus 7:26-36