Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 5

Luka 5:5-15

Help us?
Click on verse(s) to share them!
5Siman ya amsa ya ce, “Ubangiji, mun yi aiki dukan dare bamu kama komai ba, amma bisa ga maganarka, zan jefa tarun.”
6Da sun yi haka, suka kama kifaye da yawan gaske, har tarunsu suna yagewa.
7Sai suka roki abokan aikinsu da ke a dayan jirgin su zo su taimake su. Suka zo sun cika jiragen biyu da kifaye, har suka fara nutsewa.
8Amma Siman Bitrus, da ya ga haka, ya russuna a gaban Yesu, yana cewa, “Ka rabu da ni Ubangiji, gama ni mai zunubi ne.”
9Domin ya yi mamaki, da dukan wadanda suke tare da shi, sabili da yawan kifaye da suka kama.
10Wannan ya hada da Yakubu da Yahaya 'ya'yan Zabadi abokan aikin Siman. Sai Yesu ya ce wa Siman, “Kada ka ji tsoro, domin daga yanzu, za ka kama mutane.”
11Da sun kawo jiragensu waje kan kasa, suka bar komai suka kuma bi shi.
12Sa'adda yana daya daga cikin biranen, wani mutum dauke da kuturta yana nan wurin. Da ya ga Yesu, ya fadi bisa fuskarsa kasa yana rokansa, yana cewa, “Ubangji, idan ka yarda, za ka iya tsarkake ni.”
13Yesu ya mika hanunsa ya taba shi, yana cewa, “Na yarda. Ka tsarkaka.” Sai nan da nan, kuturtar ta rabu da shi.
14Ya umarce shi kada ya gaya wa kowa, amma ya ce ma sa, “Tafi ka nuna kanka ga firist sa'annan ka mika hadaya domin tsarkakewarka, kamar yadda Musa ya umarta, a matsayin shaida a garesu.”
15Amma labarinsa ya bazu nesa, taron mutane da yawa kuma suka zo wurinsa domin su ji shi, su kuma samu warkarwa daga cututtukansu.

Read Luka 5Luka 5
Compare Luka 5:5-15Luka 5:5-15