13Nan take, sai ga babban taro daga sama tare da mala'ikan suna yabon Allah, suna cewa,
14“Daukaka ga Allah daga bisa, bari salama ta kasance a duniya tsakanin mutanen da ya ke jin dadinsu.”
15Ya zama sa'adda mala'iku suka bar su zuwa cikin sama, sai makiyayan su ka ce wa junansu, “Bari mu je Baitalami mu ga wannan abin da ya faru, wanda Ubangiji ya nuna mana.”
16Su ka yi hamzari suka tafi can sun iske Maryamu da Yusufu, suka ga jaririn kuwa kwance a cikin kwamin dabbobin.
17Bayan da sun ga wannan, suka gaya wa mutane abinda aka gaya masu game da wannan yaro.
18Dukan wadanda su ka ji, su ka yi mamaki kwarai game da abin da makiyayan su ka gaya masu.
19Amma ita Maryamu ta ci gaba da tunani akan wadanan abubuwa da ta ji, tana tunani mai zurfi a cikin zuciyarta.
20Makiyayan suka koma suna ta daukaka da yabon Allah domin dukan abubuwan da suka ji, suka kuma gani, dadai da yadda aka gaya masu.
21Da ya kai kwana takwas, lokacin da za a yi wa jaririn kaciya, sai aka rada masa suna Yesu, sunan da mala'ikan ya bashi kamin a yi cikinsa.
22Da kwanakin tsarkakewar su ya wuce bisa ga shari'ar Musa, Yusufu da Maryamu suka kawo shi cikin haikali a Urushalima dominsu mika shi ga Ubangiji.
23Kamar yadda aka rubuta a dokokin Ubangiji, “Za a kira duk da na fari kebabbe ga Ubangiji.”
24Suka kuma zo su mika hadaya bisa ga yadda aka fada a shari'ar Ubangiji, “Kurciyoyi biyu ko 'yan tantabaru biyu.”
25Ga shi akwai wani mutum a Ushalima mai suna Siman. Wannan mutum adali ne kuma mai ibada. Yana jiran mai ta'aziyar Isra'ila, kuma Ruhu Mai-sarki na bisansa.
26An kuma bayyana masa ta wurin Ruhu Mai-tsarki cewa ba zai mutu ba sai ya ga Kristi na Ubangiji.
27Wata rana Siman ya zo cikin haikali ta wurin jagorar Ruhu Mai-tsarki. Da iyayen suka kawo yaron ciki, wato Yesu, domin su cika sharudan da shari'ar ke bukata,
28sai Siman ya karbe shi cikin hanuwansa, ya yabi Allah ya ce,
29“Yanzu bari bawanka ya tafi da salama, Ubangiji, bisa ga kalmarka.
30Domin idanuna sun ga cetonka,
31wanda ka shirya a gaban dukan mutane:
32Haske ne na wahayi ga al'ummai, kuma daukakar mutanenka Isra'ila.”
33Mahaifin yaron da Mahaifiyarsa, sun yi mamaki kwarai domin abubuwan da aka fada akansa.
34Sai Siman ya albarkace su ya ce wa uwatasa Maryamu, “Ki ji da kyau, wannan yaro zai zama sanadiyar faduwa da tashin mutane dayawa a Isra'ila, kuma alama wadda ake kushen ta.
35Kuma takobi zai tsaga zuciyar ki yadda tunanin mutane za ya bayyana.”
36Wata annabiya mai suna Annatu ta na nan wurin. Ita diyar Fanuyila ce daga kabilar Ashiru. Ta riga ta manyanta a shekaru sosai. Ta kasance da maigidanta shekaru bakwai bayan auren ta,
37sannan ta yi zama gwambranci na shekaru tamanin da hudu. Ba ta taba barin haikali ba, tana ci gaba da yi wa Ubangiji sujada, dare da rana.
38A dadai lokacin nan, ta hau zuwa wurinsu ta fara yi wa Allah godiya. Ta gaya wa dukan wadanda ke jiran fansar Urushalima.
39Da su ka gama komai da aka bukace su suyi bisa ga tafarkin shari'ar Ubangiji, sai suka koma Galili, zuwa birninsu, Nazarat.
40Yaron kuma ya yi girma ya zama da karfi, yana karuwa da hikima, alherin Ubangiji kuma yana kansa.
41Iyayensa sukan tafi Urushalima kowacce shekara domin idin ketarewa.
42Da yana shekara goma sha biyu, suka sake haurawa daidai lokacin idin a al'adance.
43Bayan da sun cika dukan kwanakin idin, sun fara dawowa gida. Amma dan yaron Yesu ya jinkirta ya zauna a Urushalima, kuma iyayensa basu sani ba.