Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 23

Luka 23:2-54

Help us?
Click on verse(s) to share them!
2Suka fara saransa, cewa “Mun same wannan mutum yana ruda kasarmu, ya haramta a ba Kaisar haraji, yana kuma cewa shi da kansa ne Almasihu, sarki.”
3Bilatus ya tambaye shi, cewa “Shin kaine Sarkin Yahudawa?” Sai Yesu ya amsa masa ya ce, “Haka ka ce.”
4Sai Bilatus ya ce wa manyan firistocin da taro mai yawa, “Ban samu ko laifi daya game da wannan mutumin ba.”
5Amma suka yi ta cewa, “Yana ta da hankalin mutane da koyarwa a dukan Yahudiya, ya fara daga Galili har zuwa ga wannan wuri.”
6Sa'adda Bilatus ya ji wannan, sai ya tambaya ko mutumin daga Galiline.
7Sa'adda ya gane cewa yana karkashin mulkin Hirudus, sai ya tura Yesu wurin Hirudus, wanda shi da kansa yana Urushalima a wadannan kwanakin.
8Sa'adda Hirudus ya ga Yesu, sai ya cika da farin ciki sosai, saboda ya so ganinsa tunda dadewa. Tun can ya ji game da shi sai ya yi begen ganin wadansu al'ajibai da zai yi.
9Hirudus ya tambaye Yesu cikin kalmomi masu yawa, amma Yesu bai amsa masa da komai ba.
10Sai manyan firistoci da marubuta suka tsaya, suna ta yi masa zargi mai zafi.
11Hirudus da sojojinsa suka zarge shi, suka kuma yi masa ba'a, suka sa masa tufafi masu kyau, sa'annan ya sake aika Yesu zuwa wurin Bilatus.
12Sai Hirudus da Bilatus suka zama abokai a wannan rana (da ma su abokai gaba ne).
13Bilatus ya kira manyan firistoci tare da masu mulki da kuma taron jama'ar,
14sai ya ce masu, “Kun kawo mani wannan mutum kamar wanda yake jagorar mutane ga munanan ayyuka, ku kuma gani, Ni, na tuhume shi a gabanku, ban sami ko kuskure daya daga mutumin nan game da abinda ku ke zarginsa da shi ba.
15Babu, ko Hirudus ma, ya sake komar mana da shi, kun gani, babu wani abu wanda ya yi da ya cancanci mutuwa,
16saboda haka zan yi masa horo sa'annan in sake shi.”
17Ya zama dole Bilatus ya sakar wa Yahudawa wani daurarre guda daya lokacin idin.
18Amma dukansu suka yi ihu tare, cewa, “A tafi da wannan mutumin, sai a sako mana Barabbas!”
19Barabbas mutum ne wanda aka sa a cikin kurkuku saboda wani tada hankali a cikin birni da kuma kisankai.
20Bilatus ya sake yi masu magana, yana so ya saki Yesu.
21Amma suka yi ihu, cewa, “A giciye shi, a giciye shi.”
22Sai ya sake ce masu sau na uku, “Don me, wace magunta wannan mutum ya yi? Ban sami wani abu da ya isa sanadin mutuwa game da shi ba. Saboda haka bayan na hore shi, zan sake shi.”
23Amma suka nace da murya mai karfi, suna so a giciye shi, sai muryarsu ta rinjayi Bilatus.
24Sai Bilatus ya yarda ya yi masu bisa ga abin da suke so.
25Ya sako masu wanda suka tambaya ya ba su wanda aka sa a kurkuku domin tada hankali da kuma kisankai. Amma ya ba da Yesu bisa nufinsu.
26Da suka tafi da shi, sai suka kama wani mai suna siman Bakurane, yana zuwa daga karkara, sai suka daura masa giciyen ya dauka, yana biye da Yesu.
27Babban taron jama'a, da na mata da suke makoki da kuka dominsa, suna binsa.
28Amma da ya juya wurinsu, Yesu yace, “Yan matan Urushalima, kada ku yi kuka domina, amma ku yi kuka domin kanku da 'ya'yanku.
29Gama ku gani, kwanaki suna zuwa da za su ce, 'Albarka ta tabbata ga bakararru da wadanda basu taba haihuwa ba da kuma wadanda ba a taba shan mamansu ba.'
30Sa'annan za su fara ce wa duwatsu, 'Ku fado bisanmu,' da tuddai ma, 'Ku rufe mu.'
31Gama idan sun yi wadannan abubuwan lokacin da itace yana danye, me zai faru sa'adda ya bushe?”
32Aka kai wadansu mutum biyu masu laifi, domin a kashe shi tare da su.
33Sa'adda suka zo wurin da a ke kira kwalluwa, nan suka giciye shi da barayin, daya daga hannun damansa dayan kuma daga hannun hagu.
34Yesu yace, “Uba, ka yafe masu, gama basu san abin da suke yi ba.” Sai suka jefa kuri'a, suka rarraba tufafinsa.
35Mutane sun tsaya suna kallo sa'annan masu mulki suna ta yin masa ba'a, cewa, “Ya ceci wadansu. Bari ya ceci kansa, idan shine Almasihu na Allah, zababben nan.”
36Sojojin ma suka yi masa dariya, suna zuwa wurinsa, suna mika masa ruwan tsami,
37suna cewa, “Idan kai Sarkin Yahudawa ne, ceci kanka.”
38Akwai wata alama bisansa, “Wannan shine Sarkin Yahudawa.”
39Daya daga cikin barayi wanda aka giciye, ya zage shi, cewa, “Ba kai ne Almasihu ba? Ka ceci kanka da mu.”
40Amma dayan ya amsa, ya tsauta masa cewa, “Ba ka tsoron Allah, da yake shari'arka daya ne da nasa?
41Mu kam an yi ma na daidai, gama mun samu bisa ga abin da muka yi. Amma wannan mutum bai yi wani abu mara kyau ba.”
42Sai ya kara, “Yesu, ka tuna da ni sa'adda ka shiga mulkinka.”
43Yesu ya ce masa, “Gaskiya ina ce maka, yau za ka kasance tare da ni a firdausi.”
44Anan nan a wajen sa'a na shida, sai duhu ya mamaye kasar duka har zuwa sa'a na tara
45sa'adda rana ya fadi. Sai labulen haikalin ya rabu a tsakiya zuwa kasa.
46Da kuka da murya mai karfi, Yesu yace, “Uba, na mika Ruhu na a hannunka.” Bayan da ya fadi wannan, sai ya mutu.
47Sa'adda jarumin ya ga abin da ya faru, ya daukaka Allah, cewa, “Lallai wannan mutumin mai adalci ne.”
48Sa'adda dukan taro mai yawa wadanda suka zo tare domin su shaida da idanunsu suka ga abubuwan da suka faru, suka koma suna bugan kirjinsu.
49Amma duk idon sani, da kuma matan da suka bi shi tun daga Galili, suka tsaya daga nesa, suna duban wadannan abubuwa.
50Ga shi kuwa, wani mutum mai suna Yusufu, shi dan majalisa ne, nagari ne kuma mutum mai adalci ne
51(bai yarda da shawarar da kuma abin da suka aikata ba), daga Arimatiya a kasar Yahudiya, wanda yake jiran mulkin Allah.
52Wannan mutum, ya sami Bilatus, ya tambaya a bashi jikin Yesu.
53Ya saukar da shi kasa, sai ya nade shi cikin likafani na linin mai kyau, ya kwantar da shi cikin kabari da aka sassaka shi daga dutse, inda ba a taba binne wani ba.
54Ranar kuwa, ranar shiri ce, Asabaci kuma ta kusato.

Read Luka 23Luka 23
Compare Luka 23:2-54Luka 23:2-54