Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 11

Luka 11:37-41

Help us?
Click on verse(s) to share them!
37Sa'adda ya gama jawabi, sai wani Bafarise ya ce da shi ya zo gidansa ya ci abinci, sai Yesu ya shiga ya zauna.
38Sai Bafarisen ya yi mamaki da ganin bai wanke hannu kafin ya ci abinci ba.
39Amma sai Ubangiji ya ce da shi, “Ku Farisawa kuna tsabtace bayan kofi da bangaji, amma cikin yana cike da kazamta da mugunta.
40Ku mutane marasa tunani, wanda ya yi wajen, ba shine ya yi cikin ba?
41Ku bayar da abin da ke ciki ga matalauta, kuma dukan abu zai zamar maku da tsafta.

Read Luka 11Luka 11
Compare Luka 11:37-41Luka 11:37-41