Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 9

Ayyukan Manzanni 9:26-38

Help us?
Click on verse(s) to share them!
26Sa'adda ya zo Urushalima, Shawulu ya yi niyyar hada kai da almajirai, amma dukansu suna tsoronsa, domin ba su yarda cewa shima ya zama almajiri ba.
27Amma Barnaba ya dauke shi ya kawo shi wurin manzannin. Ya kuwa gaya musu yadda Shawulu ya sadu da Ubangiji a hanya, har Ubangiji ya yi magana da shi, kuma yadda Shawulu ya yi wa'azi cikin sunan Yesu gabagadi a Dimashku.
28Ya sadu da su lokacin shigar su da fitar su a Urushalima. Ya yi wa'azi gabagadi cikin sunan Ubangiji Yesu
29kuma yana muhawara da Yahudawan Helenanci; amma sun ci gaba da kokarin kashe shi.
30Da 'yan'uwa suka gane haka, sai suka kawo shi Kaisariya, suka kuwa tura shi zuwa Tarsus.
31Sa'annan iklisiya dake dukan kasar Yahudiya, Galili da kuma Samariya suka sami salama da kuma ginuwa; suka kuwa ci gaba da tafiya cikin tsoron Ubangiji, da kuma ta'aziyar Ruhu Mai Tsarki, iklisiyar kuwa ta karu da yawan mutane.
32Har ta kai, yayin da Bitrus ya zaga dukan yankin kasar, ya dawo wurin masu bi dake zama a garin Lidda.
33A can kuwa ya sami wani mutum mai suna Iniyasu, wanda yake shanyayye ne, yana kwance har tsawon shekara takwas a kan gado.
34Bitrus ya ce masa, “Iniyasu, Yesu Almasihu ya warkar da kai. Tashi ka nade shimfidarka.” Nan take sai ya mike.
35Sai duk mazauna kasar Lidda da kasar Sarona suka ga mutumin, suka kuma juyo ga Ubangiji.
36Yanzu kuwa a Yafa akwai wata almajira, mai suna Tabita, ma'ana “Dokas.” Wannan matar kuwa tana chike da ayyukan nagarta da halin tausayi da take yi ga mabukata.
37Ya kai ga cewa a kwanakin can ta yi rashin lafiya har ta mutu; da suka wanke gawar ta suka kwantar da ita a bene.
38Da shike Lidda na kusa da Yafa, almajiran kuma sun ji cewa Bitrus yana can, suka aika mutane biyu wurinsa. Suna rokansa, “Ka zo garemu ba tare da jinkiri ba.”

Read Ayyukan Manzanni 9Ayyukan Manzanni 9
Compare Ayyukan Manzanni 9:26-38Ayyukan Manzanni 9:26-38