Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 11

Ayyukan Manzanni 11:11-16

Help us?
Click on verse(s) to share them!
11Nan da nan sai ga mutane uku tsaye a gaban gidan da muke; an aike su daga Kaisariya zuwa gare ni.
12Ruhun ya umurce ni in tafi tare da su, ba tare da nuna banbanci game da su ba. Yan'uwan nan shida sun tafi tare da ni, sai muka shiga gidan mutumin.
13Ya fada mana yadda ya ga mala'ika tsaye a cikin gidansa yana cewa “Aiki mutane zuwa Yafa, su kirawo Saminu wanda ake kira Bitrus.
14Zai gaya maku sakon da za ku sami ceto kai da dukan gidanka.”
15Da na fara magana da su, Ruhu Mai Tsarki ya sauko akansu kamar yadda ya sauko mana tun da farko.
16Sai na tuna da maganar Ubangiji, yadda ya ce, “Hakika Yahaya ya yi baptisma da ruwa, amma ku za a yi maku baptisma da Ruhu Mai Tsarki.”

Read Ayyukan Manzanni 11Ayyukan Manzanni 11
Compare Ayyukan Manzanni 11:11-16Ayyukan Manzanni 11:11-16