21Bitrus kuwa ya sauko wurin mutanen ya ce, “Ni ne wanda kuke nema. Me ya sa kuka zo?”
22Suka ce, “Shugaban soja mai suna Karniliyas, adalin mutum kuma mai bautar Allah, yana da kyakkyawar shaida a dukan al'umman Yahudawa, shi ne wanda mala'ika mai tsarki na Allah ya aika domin ka zo gidansa, ya ji sako daga wurinka.”
23Sai Bitrus ya gayyace su su zo ciki kuma su zauna tare da shi. Washegari sai ya tafi tare da su, kuma wadansu 'yan'uwa daga Yafa suka raka shi.