37Gama cikin wannan maganar take, 'Wani na shuka, wani kuma na girbi.'
38Na aike ku ku yi girbin abinda ba ku yi aiki a kai ba. Wandansu sun yi aiki, ku kuma kun shiga cikin wahalarsu.
39Yawancin Samariyawan da ke wannan birni suka gaskata da shi sabili da labarin matar data bada shaida, “Ya gaya mani duk abinda na taba yi.”
40To sa'adda Samariyawa suka zo wurinsa, sai suka roke shi ya zauna tare da su, ya kuwa zauna wurin kwana biyu.
41Wasu da dama kuma suka gaskata domin maganarsa.