1Daya daga cikin mala'ikun nan bakwai wanda ke rike da tasoshi bakwai ya zo ya ce mani, “Zo, zan nuna maka hukuncin babbar karuwarnan da ke zaune a kan ruwaye masu yawa.
2Da ita ce sarakunan duniya suka yi fasikanci. Da ruwan inabinta na fasikanci marar dacewa ta sa mazaunan duniya suka bugu.”
3Sai mala'ikan ya dauke ni cikin Ruhu ya tafi da ni jeji, sai na ga mace zaune bisa jan dabba cike da sunayen sabo. Dabbar tana da kawuna bakwai da kahonni goma.
4Matar kuwa tana sanye da tufafi na shunayya da kuma jar garura, ta kuma ci ado da kayan zinariya da duwatsu masu tamani da lu'u-lu'ai. Tana rike da kokon zinariya a hannunta cike da abubuwan kyama da na kazantar fasikancinta marar dacewa.
5Bisa goshinta an rubuta wani suna mai boyayyar ma'ana: “Babila mai girma, uwar karuwai da na kazamtattun abubuwan duniya.”
6Sai na ga matar a buge da jinin masu ba da gaskiya da kuma jinin wadanda aka kashe su domin Yesu. Da na gan ta, na yi mamaki kwarai da gaske.
7Amma mala'ikan ya ce mani, “Don me kake mamaki? Zan bayyana maka ma'anar matar da kuma na dabbar da ke dauke da ita, dabban nan da ke da kawuna bakwai da kahonni goma.
8Dabban da ka gani da, yanzu ba ta, amma ta na kusan hawowa daga rami marar iyaka. Sa'annan za ta je hallaka. Wadanda ke zaune a duniya, wadanda ba a rubuta sunayensu cikin littafin rai ba tun kafuwar duniya - za su yi mamaki idan suka ga dabbar da da ta kasance, ba ta nan yanzu, amma ta kusa zuwa.
9Wannan al'amari na bukatar hikima. Kawunnan bakwai, tuddai ne bakwai da macen ke zaune a kai.
10Su kuma sarakuna ne bakwai. Sarakuna biyar sun fadi, daya na nan, amma dayan bai zo ba tukuna; sa'anda ya zo zai kasance na dan lokaci kadan.
11Dabban da ya kasance a da, amma yanzu ba shi, shi ma sarki ne na takwas; amma shi daya ne cikin sarakunan nan bakwai, kuma zai tafi hallaka.
12Kahonnin nan goma da ka gani sarakuna goma ne wadanda ba a nada su ba tukuna, amma za su karbi iko kamar na sarakai na sa'a daya tare da dabban.
13Ra'ayinsu daya ne, za su ba da sarautarsu da ikon su ga dabban.
14Za su yi yaki da Dan Rago. Dan Ragon zai ci nasara a kansu domin shi Ubangijin iyayengiji ne da Sarkin sarakuna - kuma tare da shi sune kirayayyun, zababbun, amintattun.”
15Mala'ikan ya ce mani, “Ruwayen da ka gani, inda karuwar ke zaune, jama'a ce, da taro masu dumbin yawa, da al'ummai da harsuna.
16Kahonnin nan goma da ka gani - su da dabban za su ki karuwar. Za su washe ta su tsiranceta, za su lankwame namanta, za su kone ta gaba daya da wuta.
17Gama Allah ya sa a zukantansu su yi nufinsa ta wurin amincewarsa, su sadaukar da ikonsu na yin mulki ga dabban har sai maganar Allah ta cika.
18Matar da ka gani ita ce babban birnin nan da ke mulki bisa sarakunan duniya.”