Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Wahayin Yahaya

Wahayin Yahaya 14

Help us?
Click on verse(s) to share them!
1Sai na duba na ga Dan Ragon yana tsaye a kan Dutsen Sihiyona. Tare da shi akwai mutum dubu dari da arba'in da hudu wadanda aka rubuta sunansa da sunan Ubansa a goshinsu.
2Na ji wata murya daga sama mai kara kamar kogin ruwa mai gudu da kuma aradu mai kara. Muryar da na ji ta yi kama da masu molo suna kada molonsu.
3Suka raira sabuwar waka a gaban kursiyin da kuma gaban rayayyun halittun nan hudu, da kuma dattawan. Ba mai iya koyon wakar nan sai dai mutum 144, 000 nan wadanda aka fanso daga duniya.
4Wadannan sune wadanda basu kazantar da kansu da mata ba, gama sun kebe kansu da tsarki daga halin jima'i. Wadannan ne ke bin Dan Ragon duk inda ya tafi. Aka fanso su daga cikin mutane domin su zama nunan fari domin Allah da Dan Ragon.
5Ba a iske karya a bakinsu ba; ba su da aibi.
6Na ga wani mala'ika na firiya a tsakiyar sararin sama, wanda yake da madawwamin sako na labari mai dadi domin a sanar da ita ga mazaunan duniya - ga kowacce al'umma, da kabila, da harshe, da kuma jama'a.
7Yayi kira da babbar murya, “Ku ji tsoron Allah, ku daukaka shi. Gama sa'arsa ta hukunci ta yi. Yi masa sujada, shi wanda ya yi sama da kasa, da teku, da kuma mabulbular ruwa.”
8Sai wani malai'ka, malaika na biyu, ya biyo yana cewa, “Ta fadi, Babila mai girma ta fadi, wadda ta rinjayi dukan al'ummai su sha ruwan inabin fasikancinta.”
9Wani mala'ika - na uku - ya biyo su da murya mai karfi yana cewa, “Duk wanda ya yi sujada ga dabban da kuma siffarsa, ya karbi alama a goshinsa ko a hannunsa,
10shi ma zai sha daga ruwan inabin fushin Allah, ruwan inabi da aka zuba tsantsa cikin kokon fushinsa. Wanda ya sha shi za a azabtar da shi da wuta, da farar wuta, a gaban tsarkakan mala'ikun Allah da kuma Dan Ragon.
11Hayaki daga azabarsu yana tashi sama har abada abadin, kuma ba su da hutu dare ko rana - wadannan masu sujada ga dabban da siffarsa da kuma dukan wadanda suka karbi alamar sunansa.
12Wannan shine kira domin hakurin jimrewa na wadanda ke da tsarki, wadanda suke biyayya ga dokokin Allah da bangaskiya cikin Yesu.”
13Na ji murya daga sama cewa, “Rubuta wannan: Masu albarka ne matattu da suka mutu cikin Ubangiji.” Ruhu yace, 'I' domin sun huta daga wahalarsu, gama ayyukansu na biye da su.”
14Na duba sai ga farin gajimare. Zaune a kan gajimaren akwai wani kamar Dan Mutum. Yana da kambin zinariya a kansa da lauje mai kaifi a hannunsa.
15Sai wani malaika ya fito daga haikalin, ya yi kira da murya mai karfi ga wanda ke zaune kan gajimare: “Dauki laujenka ka fara girbi, domin lokacin girbin duniya ya yi.”
16Sai wanda ke zaune a kan gajimaren ya wurga laujensa bisa kan duniya, aka kuma girbe duniya.
17Wani mala'ika ya fito daga haikali a sama, shi ma yana da kakkaifan lauje.
18Sai wani mala'ika ya fito daga bagadin kona turare, wanda yake da iko kan wutar. Ya yi kira da murya mai karfi ga wanda yake rike da kakkaifan lauje, “Ka dauki kakkaifan laujenka ka tattara nonnan innabi daga itacen inabin na duniya, gama inabin ya nuna.”

19Mala'ikan ya jefa laujensa duniya ya tattara girbin inabin duniya. Ya zuba shi a cikin babbar taskar wurin matsar ruwan inabi na fushin Allah.
20Aka tattake wurin matsar inabin a bayan birni, jini ya yi ta gudu daga wurin matsar inabin, ya kai kamar tsawon linzami a bakin doki, har mil dari biyu.