Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Markus - Markus 5

Markus 5:24-36

Help us?
Click on verse(s) to share them!
24Sai ya tafi tare da shi, babban taro suka biyo shi har ma suna matse shi.
25Akwai wata mace wadda ta ke zubar jini ta kai tsawon shekara goma sha biyu.
26Ta sha wahala kwarai da gaske ta je wurin likitoci da yawa ta kashe kudi sosai, amma ba ta warke ba abin ma sai karuwa ya ke yi.
27Ta ji labarin Yesu. Sai ta biyo bayansa yana tafiya cikin taro, ta taba habar rigarsa.
28Domin ta ce “Idan dai na taba ko da habar rigarsa zan warke.”
29Da dai ta taba shi sai zubar jinin ta ta tsaya, ta ji a jikin ta ta warke, daga damuwarta.
30Nan da nan, Yesu ya ji iko ya fita daga gare shi sai ya ce “wanene ya taba rigata?”
31Almajiransa suka ce, “a cikin wannan taron mutane da yawa ka ce wanene ya taba ni?”
32Amma Yesu ya waiga ya ga ko wanene ya taba shi.
33Matar ta san abin da ya faru sai ta zo cikin tsoro da rawar jiki ta durkusa a gaban Yesu ta fada masa gaskiya.
34Sai ya ce da ita, “Diya bangaskiyarki ta warkar da ke, ki tafi lafiya kin sami warkewa daga cutarki”.
35Sa'adda ya ke magana da ita sai ga mutane daga gidan shugaban majami'a suka ce “Diyarka ta mutu me ya sa za ka dami malam?”
36Amma sa'adda Yesu ya ji abin da suka ce, sai ya ce da shugaban majami'ar, “kada ka ji tsoro ka ba da gaskiya kawai.”

Read Markus 5Markus 5
Compare Markus 5:24-36Markus 5:24-36