Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 12

Luka 12:18-56

Help us?
Click on verse(s) to share them!
18Sai ya ce, na san abin da zan yi. Zan rushe rumbuna na in gina wadansu manya-manya, a nan zan ajjiye hatsi na da dukan abubuwa.
19Sai in ce da raina, “Ya raina, kana da abu da yawa da aka ajjiye dominka, sai ka huta, ka ci, ka sha, ka yi murna.”
20Amma sai Allah ya ce da shi, 'Wawan mutum, a cikin daren nan ana son ranka daga wurinka. Kayan da ka tara ka shirya wa kanka, na wa za su zama?'
21Haka wanda ya tara wa kansa dukiya yake, idan ba shi da dukiya a wurin Allah.”
22Yesu, ya ce da almajiransa, “Saboda haka ina cewa da ku, kada ku damu da rayuwarku, wato, abin da za ku ci, ko abin da za ku sa a jikinku.
23Gama rai ya fi abinci, jiki kuma ya fi tufafi.
24Ku dubi hankaki wadanda ba sa yin shuka, ba sa yin girbi. Ba su da rumbuna ko dakunan ajjiya, amma Allah ya na ciyar da su. Ku fa kun fi tsuntsaye daraja!
25Wanene a cikinku ta wurin sha'awarsa za ya iya karawa kansa kwanaki?
26Idan ba ku iya yi wa kanku dan karamin abu ba, me ya sa za ku damu da sauran abubuwa?
27Ku dubi furanni a daji - yadda suke yin girma. Ba su kan yi aiki ba, ba su kan yi kadi ba. Ina gaya maku, ko Sulaimanu, a cikin darajarsa, bai sa tufafin da suka fi nasu kyau ba.
28Idan Allah ya sa wa ciyawa tufafi masu kyau haka, wadda yau tana nan, gobe kuma a sa ta a wuta, ta yaya zai kasa sa maku tufafi, ku masu kankantar bangaskiya!
29Kada ku damu da abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kuma kada ku yi alhini.
30Gama dukan al'umman duniya suna neman wadannan abubuwa, kuma Ubanku ya san kuna bukatar wada nan abubuwan.
31Amma ku bidi mulkinsa, wadannan abubuwa kuma za a kara maku su.
32Kada ku ji tsoro, ku 'yan kanana, domin da murna Ubanku zai ba ku mulkin.
33Ku sayar da abin da ku ke da shi ku ba matalauta. Kuyi wa kanku jakukkuna wadanda ba za su lalace ba, ku yi ajjiya cikin sama inda abin ba ya karewa, inda barayi ba za su iya zuwa ba, kwari kuma ba za su iya lalatawa ba.
34Domin inda dukiyarka take, can zuciyarka za ta kasance kuma.
35Ku rage tsawon tufafinku, ku yi dammara, ya zama fitilarku tana ci koyaushe,
36ku kuma zama kamar wadanda suke jiran mai gidansu ya dawo daga gidan buki, domin duk sa'adda ya zo ya kwankwasa kofa, nan da nan za su bude masa.
37Masu albarka ne wadannan bayi, wadanda ubangijinsu za ya tarar suna jiran dawowar sa. Gaskiya ni ke gaya ma ku, zai yi dammara yasa su zazzauna ya ba su abinci shi da kansa.
38Ko da ubangijinsu ya zo da dare, ko da tsakar dare, ya tarar da su a shirye suna jiransa. Masu albarka ne wadannan bayi.
39Kuma ku san wannan, da mai gida ya san lokacin da barawo zai zo, ba zai bari a fasa masa gida a shiga ba.
40Sai ku zauna da shiri fa domin ba ku san lokacin da Dan Mutum zai dawo ba.”
41Sai Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, mu ka ke fadawa wannan misali, ko ga kowa da kowa ne?”
42Sai Ubangiji ya ce, “Wanne shugaba ne, mai aminci, mai hikima kuma wanda ubangijinsa za ya damka bayinsa a hannunsa, domin ya kula da su, ya ba su abincinsu a kan lokaci?
43Mai albarka ne wannan bawa, wanda ubangijinsa za ya tarar da shi yana yin abin da aka sa shi ya yi.
44Hakika, ina gaya maku, zai danka dukan malakarsa a gareshi.
45Amma idan wannan bawa, ya ce a cikin zuciyarsa, 'Ubangiji na yayi jinkirin dawowa,' sai ya fara dukan bayin, maza da mata abokan bautarsa, ya ci ya sha, ya bugu,
46ubangijin bawan nan zai dawo a lokacin da bawan bai sa tsammani ba, kuma a cikin lokacin da bai sani ba, ya daddatsa shi gunduwa-gunduwa, ya kuma hada shi da marasa aminci.
47Bawan nan, ya san halin ubagijinsa, amma bai shirya yayi abin da ubangijinsa yake so ba. Zai sha duka da bulala da yawa.
48Amma shi wanda bai sani ba, kuma yayi abin da ba daidai ba, ba zai sha duka da bulala da yawa ba. Dukan wanda aka ba abu da yawa, za a kuma nemi abu da yawa daga wurinsa. Kuma ga wanda aka ba abu da yawa amana, za a nemi abu mafi yawa daga gareshi.
49Na zo domin in sa wuta a duniya, na so da ta riga ta kama.
50Amma ni, ina da baftisma wadda za a yi mani baftisma da ita, kuma na kagara, da an riga an yi ta!
51Kuna zaton na zo duniya domin in kawo salama? Na ce maku a'a, amma tsattsaguwa.
52Daga yanzu za a sami mutane biyar a cikin gida daya, kuma za su rarrabu, mutane uku suna gaba da biyu, biyun kuma suna gaba da ukun.
53Da da mahaifi za su yi gaba da juna, dan zai yi gaba da mahaifinsa. Mahaifiya za ta yi gaba da diyarta, diya kuma gaba da mahafiyarta; uwar miji za ta yi gaba da matar danta, matar da kuma gaba da uwar mijinta.”
54Yesu, ya kuma gaya wa taron, “Da kun ga hadari ya taso daga yamma, nan da nan sai ku ce za a yi ruwa, haka kuwa ya kan zama.
55Idan iska tana busowa daga kudu sai ku ce za a yi zafi mai tsanani, haka kuwa ya kan faru.
56Munafukai, kun iya fasarta yanayin kasa da sama, amma baku iya fasarta abin da yake faruwa yanzu ba?

Read Luka 12Luka 12
Compare Luka 12:18-56Luka 12:18-56