11Yahudawa da tubabbun cikin Yahudanci, Kiretawa da Larabawa, duk munji su suna fadi a harshenmu game da manyan ayyukan Allah.”
12Dukansu suka yi mamaki suka rikice; suka ce da junansu, “Menene ma'anar wannan?”
13Amma wasu suka yi ba'a suka ce, “Sun bugu ne da sabon ruwan inabi.”
14Amma Bitrus ya tashi tare da sha dayan, ya daga murya ya ce da su, “Mutanen Yahuda da dukanku dake zaune a Urushalima, bari ku san wannan; ku saurari maganata.
15Domin wadannan mutanen ba buguwa suka yi ba yadda kuke zato, domin yanzu karfe tara ne na safe kawai.