31Saboda haka ku yi lura. Ku tuna da cewa shekara uku ban fasa yi wa kowannenku gargadi da hawaye dare da rana ba.
32Yanzu ina mika ku ga Allah, da maganar Alherinsa, wadda take da ikon gina ku ta kuma ba ku gado tare da dukan wadanda ke cikin kebabbu na Allah.
33Ban yi kyashin azurfa, ko zinariya, ko tufafin wani ba.