1Ya ku 'yan'uwana, muddin kuna rike da bangaskiyar ku ga Ubangijinmu Yesu Almasihu, Ubangijin daukaka, kada ku nuna bambanci ga wadansu mutane.
2Idan wani mutum ya halarci taron ku da zobban zinariya da tufafi masu kyau, wani matalauci kuma ya shigo da tufafi marasa tsabta.
3Sa'adda kuka kula da mai tufafi masu kyau nan, har kuka ce masa, “Idan ka yarda ka zauna a nan wuri mai kyau,” mataulacin nan kuwa kuka ce masa, “Kai ka tsaya daga can,” ko kuwa, “Zauna a nan kasa a gaba na,”
4Ashe ba kuna zartar da hukunci a tsakanin ku ba ke nan? Ba kun zama alkalai na mungayen tunani kenan ba?
5Ku saurara, ya 'yan'uwana kaunatattu, ashe, Allah bai zabi matalautan duniyar nan su zama mawadata cikin bangaskiya ba, su kuma zama magada a cikin mulkin nan da ya yi wa masu kaunar sa alkawari ba?
6Amma, kun wulakanta matalauta! Ashe, ba masu arzikin ne suke matsa maku ba? Ba su ne kuwa suke jan ku zuwa gaban shari'a ba?
7Ba kuma sune ke sabon sunan nan mai girma da ake kiran ku da shi ba?
8Duk da haka, idan kuka cika muhimmiyar shari'ar da nassi ya ce, “Ka kaunaci makwabcin ka kamar kanka,” to, madalla.
9Amma in kun nuna bambanci, kun yi zunubi kenan, shari'a ta same ku da laifin keta umarni.
10Duk wanda yake kiyaye dukan shari'a, amma ya yi tuntube a hanya daya kadai, ya sabi shari'a gaba daya ke nan.
11Domin wanda ya ce, “Kada ka yi zina,” shi ne kuma ya ce, “Kada ka yi kisan kai.” Idan ba ka yi zina ba amma ka yi kisan kai, ai, ka zama mai taka shari'a kenan.
12Saboda haka, ku yi magana ku kuma yi aiki kamar wadanda za a hukunta ta wurin 'yantacciyar shari'a.
13Gama hukunci yana zuwa ba tare da jinkai ba ga wadanda ba su nuna jinkai. Jinkai ya yi nasara a kan hukunci.
14Ina amfanin haka, 'yan'uwana, idan wani ya ce yana da bangaskiya, kuma ba shi da ayyuka? Wannan bangaskiyar ba za ta cece shi ba, ko za ta iya?
15Misali, idan wani dan'uwa ko 'yar'uwa ba su da tufa mai kyau ko suna rashin abincin yini.
16Misali, idan waninku kuma ya ce masu, “Ku tafi cikin salama, ku kasance da dumi ku koshi.” Idan baku ba su abubuwan da jiki ke bukata ba, ina amfanin wannnan?
17Haka ma, bangaskiya ita kadai, ba tare da aikin da ya nuna ta ba, matacciya ce.
18To, wani zai ce, “Ai, kai kana da bangaskiya, ni kuwa ina da ayyuka.” Nuna mani bangaskiyar ka ba tare da ayyuka ba, ni kuma in nuna maka bangaskiya ta ta wurin ayyuka na.
19Ka gaskanta cewa Allah daya ne; ka yi daidai. Amma ko aljannu ma sun gaskata, kuma suna rawar jiki.
20Kana so ka sani, kai marar azanci, cewa bangaskiya ba tare da ayyuka ba banza ce?
21Ba an baratar da Ibrahim mahaifinmu ta wurin ayyuka ba, sa'adda ya mika Ishaku dansa a bisa bagadi?
22Ka gani, ashe, bangaskiyar sa ta yi aiki da ayyukan sa, kuma da cewa ta wurin ayyuka bangaskiyar sa ta ginu sosai.
23Nassi kuma ya cika da ya ce, “Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lisafta masa ita a matsayin adalci.” Aka kuma kira shi abokin Allah.
24Kun ga, ta wurin ayyuka ne mutum yake samu baratarwa ba ta wurin bangaskiya kadai ba.
25Ta wannan hanyar kuma, ba Rahab karuwar nan ta samu baratarwa ta wurin ayyuka, da ta marabci masu leken asirin nan ta fitar da su ta wata hanya dabam ba?
26Kamar yadda jiki idan ba tare da ruhu ba matacce ne, haka kuma, bangaskiya ba tare da ayyuka ba matacciya ce.