Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yakubu - Yakubu 1

Yakubu 1:1-7

Help us?
Click on verse(s) to share them!
1Yakubu, bawan Allah, da kuma Ubangiji Yesu Almasihu, zuwa ga kabilun nan goma sha biyu da suke warwatse: ina gaishe ku.
2Ku dauke su duka da farin ciki, 'yan'uwana, duk sa'adda kuke fuskantar jarabobi.
3Ku sani cewa gwajin banskiyar ku ta kan haifi jimiri.
4Bari jimiri ya cika aikin sa, domin ku kai ga cikakken girma kuma ku kammalu, domin kada ku rasa komai.
5Amma idan waninku yana bukatar hikima, sai ya roki Allah, wanda yake bayarwa a yalwace, ba tare da gori ba ga duk wanda ya roke shi, zai kuwa ba shi.
6Amma fa sai ya roka da banskiya ba tare da shakka ba, don mai shakka kamar rakumin ruwan teku yake, wanda iska take korarwa tana tunkudawa.
7Tilas ne wannan mutum kada ya yi tunanin zai karbi wani abu a wurin Ubangiji.

Read Yakubu 1Yakubu 1
Compare Yakubu 1:1-7Yakubu 1:1-7