Text copied!
Bibles in Hausa

Yahaya 8:11-19 in Hausa

Help us?

Yahaya 8:11-19 in Litafi Mai-tsarki

11 Ta ce, “Ba kowa, Ubangiji” Yesu ya ce, “Ni ma ban kashe ki ba. Ki yi tafiyar ki, daga yanzu kada ki kara yin zunubi.”
12 Yesu ya kara yin magana da mutanen cewa, “Ni ne hasken duniya, shi wanda ya biyo ni, ba zai yi tafiya cikin duhu ba, amma za ya sami hasken rai.
13 Farisawa suka ce masa, “Kana bada shaida a kan ka, shaidarka ba gaskiya ba ce.”
14 Yesu ya amsa ya ce masu, “Ko ma na bada shaida a kai na, shaidata gaskiya ce, na san daga inda na fito da inda zan tafi, amma ku baku san daga inda na fito ba, baku kuma san inda zan tafi ba.
15 Kuna shari'a ta son kai, ni ko ban yi wa kowa shari'a ba.
16 Ko ma da na yi shari'a, shari'ata gaskiya ce domin ba ni kadai ba ne, amma ina tare da Uba wanda ya aiko ni.
17 I, a cikin dokarku an rubuta cewa shaidar mutum biyu gaskiya ce.
18 Ni ne ni ke shaidar kaina, kuma Uba wanda ya aiko ni ya na shaida ta.
19 Su ka ce da shi, “Ina ubanka?” Yesu ya amsa ma su ya ce, “baku san ni ba balle Ubana, in da kun san ni da kun san Uba na kuma.”
Yahaya 8 in Litafi Mai-tsarki