Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 8

Yahaya 8:11-19

Help us?
Click on verse(s) to share them!
11Ta ce, “Ba kowa, Ubangiji” Yesu ya ce, “Ni ma ban kashe ki ba. Ki yi tafiyar ki, daga yanzu kada ki kara yin zunubi.”
12Yesu ya kara yin magana da mutanen cewa, “Ni ne hasken duniya, shi wanda ya biyo ni, ba zai yi tafiya cikin duhu ba, amma za ya sami hasken rai.
13Farisawa suka ce masa, “Kana bada shaida a kan ka, shaidarka ba gaskiya ba ce.”
14Yesu ya amsa ya ce masu, “Ko ma na bada shaida a kai na, shaidata gaskiya ce, na san daga inda na fito da inda zan tafi, amma ku baku san daga inda na fito ba, baku kuma san inda zan tafi ba.
15Kuna shari'a ta son kai, ni ko ban yi wa kowa shari'a ba.
16Ko ma da na yi shari'a, shari'ata gaskiya ce domin ba ni kadai ba ne, amma ina tare da Uba wanda ya aiko ni.
17I, a cikin dokarku an rubuta cewa shaidar mutum biyu gaskiya ce.
18Ni ne ni ke shaidar kaina, kuma Uba wanda ya aiko ni ya na shaida ta.
19Su ka ce da shi, “Ina ubanka?” Yesu ya amsa ma su ya ce, “baku san ni ba balle Ubana, in da kun san ni da kun san Uba na kuma.”

Read Yahaya 8Yahaya 8
Compare Yahaya 8:11-19Yahaya 8:11-19