Text copied!
Bibles in Hausa

Yahaya 20:8-24 in Hausa

Help us?

Yahaya 20:8-24 in Litafi Mai-tsarki

8 Sai almajirin nan da ya riga isa kabarin shi ma ya shiga ya gani, sai ya ba da gaskiya.
9 Har ya zuwa wannan lokacin basu san nassin daya ce zai tashi daga matattu ba.
10 Sai almajiran suka sake komawa gida kuma.
11 Amma Maryamu tana tsaye a bakin kabarin tana kuka. Yayin da take kuka, sai ta sunkuya ta leka cikin kabarin.
12 Sai ta ga mala'iku guda biyu cikin fararen kaya zaune, daya ta wurin kai daya kuma ta wurin kafafu inda aka kwantar da Yesu.
13 Sukace mata, “Uwargida don me kike kuka? Sai tace masu, “Domin sun dauke Ubangijina, ban kuwa san inda suka ajiye shi ba.
14 Bayan ta fadi haka, ta juya sai ta ga Yesu tsaye a wurin. Amma bata san cewa Yesu bane,
15 Yesu yace mata, “Uwargida, me yasa kike kuka? Wa kuma kike nema? Domin tana zaton shine mai kula da lambun, sai tace masa, “Maigida in kaine ka dauke shi, gaya mani inda ka sa shi, ni kuwa in dauke shi.”
16 Yesu yace mata, “Maryamu”. Sai ta juya, tace masa da Armaniyanci “Rabboni!” wato mallam.
17 Yesu yace mata, kada ki taba ni, domin har yanzu ban hau wurin Uba ba tukuna, amma kije wurin 'yan'uwana kice masu, zan je wurin Ubana da Ubanku, Allahna da kuma Allahnku”.
18 Maryamu Magadaliya ta je tace wa almajiran, “Na ga Ubangiji” Ta kuma ce ya fada mata wadannan abubuwa.
19 Da yamma a wannan rana, a rana ta farko ta mako, almajiran suna kulle a daki saboda tsoron Yahudawa, Yesu yazo ya tsaya a tsakaninsu, yace “Salama Agareku”.
20 Bayan ya fadi haka, sai ya nuna masu hannuwansa da kuibinsa. Da almajiran suka ga Ubangiji, sai suka yi farin ciki.
21 Yesu ya sake ce masu, “salama agareku. “Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka Ni ma na aike ku”.
22 Da Yesu ya fadi haka, sai ya hura masu lumfashinsa, yace masu, “Ku karbi Ruhu Mai Tsarki.
23 Duk wanda kuka gafarta wa zunubai, an gafarta masa; kowa kuka rike zunubansa, an rikesu.”
24 Toma, daya daga cikin sha biyun, wanda ake kira Dan Tagwai, baya tare dasu lokacin da Yesu ya bayyana.
Yahaya 20 in Litafi Mai-tsarki