Text copied!
Bibles in Hausa

Yahaya 20:13-31 in Hausa

Help us?

Yahaya 20:13-31 in Litafi Mai-tsarki

13 Sukace mata, “Uwargida don me kike kuka? Sai tace masu, “Domin sun dauke Ubangijina, ban kuwa san inda suka ajiye shi ba.
14 Bayan ta fadi haka, ta juya sai ta ga Yesu tsaye a wurin. Amma bata san cewa Yesu bane,
15 Yesu yace mata, “Uwargida, me yasa kike kuka? Wa kuma kike nema? Domin tana zaton shine mai kula da lambun, sai tace masa, “Maigida in kaine ka dauke shi, gaya mani inda ka sa shi, ni kuwa in dauke shi.”
16 Yesu yace mata, “Maryamu”. Sai ta juya, tace masa da Armaniyanci “Rabboni!” wato mallam.
17 Yesu yace mata, kada ki taba ni, domin har yanzu ban hau wurin Uba ba tukuna, amma kije wurin 'yan'uwana kice masu, zan je wurin Ubana da Ubanku, Allahna da kuma Allahnku”.
18 Maryamu Magadaliya ta je tace wa almajiran, “Na ga Ubangiji” Ta kuma ce ya fada mata wadannan abubuwa.
19 Da yamma a wannan rana, a rana ta farko ta mako, almajiran suna kulle a daki saboda tsoron Yahudawa, Yesu yazo ya tsaya a tsakaninsu, yace “Salama Agareku”.
20 Bayan ya fadi haka, sai ya nuna masu hannuwansa da kuibinsa. Da almajiran suka ga Ubangiji, sai suka yi farin ciki.
21 Yesu ya sake ce masu, “salama agareku. “Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka Ni ma na aike ku”.
22 Da Yesu ya fadi haka, sai ya hura masu lumfashinsa, yace masu, “Ku karbi Ruhu Mai Tsarki.
23 Duk wanda kuka gafarta wa zunubai, an gafarta masa; kowa kuka rike zunubansa, an rikesu.”
24 Toma, daya daga cikin sha biyun, wanda ake kira Dan Tagwai, baya tare dasu lokacin da Yesu ya bayyana.
25 Sauran almajiran sukace masa “Mun ga Ubangiji”. Sai yace masu, “In ban ga gurbin kusoshi a hannuwansa ba, in sa yatsana a gurbin kusoshin ba, in kuma sa hannuna cikin kuibinsa ba, ba zan bada gaskiya ba.
26 Bayan kwana takwas har wa yau almajiran na cikin gida, Toma ma na tare dasu, kofofin suna kulle, sai ga Yesu a tsakaninsu yace, “Salama agareku”.
27 Sa'an nan yace wa Toma, “Iso nan da yatsanka, dubi hannuwana. Miko hannunka kuma kasa a kuibina, kada ka zama marar bada gaskiya, sai dai, mai bada gaskiya”.
28 Toma ya amsa yace “Ya Ubangijina da Allahna!”
29 Yesu yace masa, “Wato saboda ka gan ni, ka bada gaskiya? Albarka ta tabbata ga wadanda basu gani ba, amma kuwa sun bada gaskiya.
30 Yesu yayi wadansu alamu da yawa dabam dabam a gaban almajiransa, wadanda ba'a rubuta a littafin nan ba.
31 Amma an rubuta wadannan ne, domin ku bada gaskiya Yesu shine Almasihu, Dan Allah, ta wurin gaskatawa kuma ku sami rai cikin sunansa.
Yahaya 20 in Litafi Mai-tsarki