Text copied!
Bibles in Hausa

Romawa 8:2-18 in Hausa

Help us?

Romawa 8:2-18 in Litafi Mai-tsarki

2 Domin ka'idar ruhun rai a cikin Almasihu Yesu ta maishe mu 'yanttatu daga ka'idar zunubi da mutuwa.
3 Saboda abin da shari'a bata iya aikatawa ba domin kasawa ta wurin jiki, Allah ya yi. Ya aiko da dansa a kamanin jiki mai zunubi domin ya zama hadaya domin zunubi, sai ya yi Allah wadai da zunubi a cikin jiki.
4 Ya yi haka domin bukatar shari'a ta sami cika a cikinmu, mu da muke tafe ba ta gwargwadon jiki ba, amma ta gwargwadon ruhaniya.
5 Wadanda ke rayuwa gwargwadon jiki sukan lura da al'amuran jiki, amma su da ke rayuwa a gwargwadon Ruhu sukan mai da hankali ga al'amuran Ruhu.
6 To kwallafa rai ga jiki mutuwa ce, amma kwallafa rai ga Ruhu rai ne da salama.
7 Haka yake domin kwallafa rai ga jiki gaba yake da Allah, gama baya biyyaya ga shari'ar Allah, balle ma ya iya.
8 Wadanda ke a jiki ba su iya faranta wa Allah zuciya.
9 Duk da haka, ba ku cikin jiki amma a cikin Ruhu, idan gaskiya ne, Ruhun Allah na rayuwa cikinku. Amma idan wani ba shi da Ruhun Almasihu, shi ba na sa bane.
10 In Almasihu na cikinka, jikin ka fa matacce ne ga zunubi, amma ruhu na rayuwa bisa ga adalci.
11 Idan Ruhun wanda ya tada Yesu daga matattu na raye a cikinku, to shi wanda ya tada Almasihu da ga matattu za ya bada rai ga jikinku masu matuwa ta wurin Ruhunsa, da ke rayuwa a cikin ku.
12 To, 'yan' uwa, muna da hakki amma ba bisa jiki ba, da za mu yi rayuwa bisa ga dabi'ar jiki.
13 Gama idan kun yi rayuwa gwargwadon jiki, za ku mutu kenan, amma idan ta wurin Ruhu ku ka kashe ayyukan jiki, za ku rayu.
14 Gama duk wadanda Ruhun Allah ke bishe su, su 'ya 'yan Allah ne.
15 Gama ba ku karbi ruhun bauta da ke sa tsoro ba. Maimakon haka, kun karbi ruhun diyanci, ta wurinsa muke tadda murya muna kira, “Abba, Uba!”
16 kansa na bada shaida tare da namu ruhun cewa mu 'ya'yan Allah ne.
17 Idan mu 'ya'ya ne, ai mu magada ne kenan, magadan Allah. Kuma mu magada ne tare da Almasihu, hakika idan mun sha wahala tare da shi za a kuma daukaka mu tare da shi.
18 Gama na yi la'akari cewa wahalonin zamanin nan ba su isa a kwatanta su da daukakar da za'a bayyana mana ba.
Romawa 8 in Litafi Mai-tsarki