Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Romawa - Romawa 8

Romawa 8:2-18

Help us?
Click on verse(s) to share them!
2Domin ka'idar ruhun rai a cikin Almasihu Yesu ta maishe mu 'yanttatu daga ka'idar zunubi da mutuwa.
3Saboda abin da shari'a bata iya aikatawa ba domin kasawa ta wurin jiki, Allah ya yi. Ya aiko da dansa a kamanin jiki mai zunubi domin ya zama hadaya domin zunubi, sai ya yi Allah wadai da zunubi a cikin jiki.
4Ya yi haka domin bukatar shari'a ta sami cika a cikinmu, mu da muke tafe ba ta gwargwadon jiki ba, amma ta gwargwadon ruhaniya.
5Wadanda ke rayuwa gwargwadon jiki sukan lura da al'amuran jiki, amma su da ke rayuwa a gwargwadon Ruhu sukan mai da hankali ga al'amuran Ruhu.
6To kwallafa rai ga jiki mutuwa ce, amma kwallafa rai ga Ruhu rai ne da salama.
7Haka yake domin kwallafa rai ga jiki gaba yake da Allah, gama baya biyyaya ga shari'ar Allah, balle ma ya iya.
8Wadanda ke a jiki ba su iya faranta wa Allah zuciya.
9Duk da haka, ba ku cikin jiki amma a cikin Ruhu, idan gaskiya ne, Ruhun Allah na rayuwa cikinku. Amma idan wani ba shi da Ruhun Almasihu, shi ba na sa bane.
10In Almasihu na cikinka, jikin ka fa matacce ne ga zunubi, amma ruhu na rayuwa bisa ga adalci.
11Idan Ruhun wanda ya tada Yesu daga matattu na raye a cikinku, to shi wanda ya tada Almasihu da ga matattu za ya bada rai ga jikinku masu matuwa ta wurin Ruhunsa, da ke rayuwa a cikin ku.
12To, 'yan' uwa, muna da hakki amma ba bisa jiki ba, da za mu yi rayuwa bisa ga dabi'ar jiki.
13Gama idan kun yi rayuwa gwargwadon jiki, za ku mutu kenan, amma idan ta wurin Ruhu ku ka kashe ayyukan jiki, za ku rayu.
14Gama duk wadanda Ruhun Allah ke bishe su, su 'ya 'yan Allah ne.
15Gama ba ku karbi ruhun bauta da ke sa tsoro ba. Maimakon haka, kun karbi ruhun diyanci, ta wurinsa muke tadda murya muna kira, “Abba, Uba!”
16kansa na bada shaida tare da namu ruhun cewa mu 'ya'yan Allah ne.
17Idan mu 'ya'ya ne, ai mu magada ne kenan, magadan Allah. Kuma mu magada ne tare da Almasihu, hakika idan mun sha wahala tare da shi za a kuma daukaka mu tare da shi.
18Gama na yi la'akari cewa wahalonin zamanin nan ba su isa a kwatanta su da daukakar da za'a bayyana mana ba.

Read Romawa 8Romawa 8
Compare Romawa 8:2-18Romawa 8:2-18