Text copied!
Bibles in Hausa

Romawa 7:20-23 in Hausa

Help us?

Romawa 7:20-23 in Litafi Mai-tsarki

20 To idan na yi abin da ba ni so in aikata, wato kenan ba ni bane ke aikatawa, amma zunubin da ke zaune a cikina.
21 Don haka, sai na iske, akwai ka'ida a cikina dake son aikata abu mai kyau, amma kuma ainihin mugunta na tare dani.
22 Domin a cikina ina murna da shari'ar Allah.
23 Amma ina ganin wasu ka'idoji daban a gabobin jikina, su na yaki da wannan sabuwar ka'idar da ke cikin tunanina, suna kuma sanya ni bauta ta wurin ka'idar zunubi wadda ke cikin gabobin jikina.
Romawa 7 in Litafi Mai-tsarki