Text copied!
Bibles in Hausa

Romawa 3:5-27 in Hausa

Help us?

Romawa 3:5-27 in Litafi Mai-tsarki

5 Amma idan rashin adalcinmu ya nuna adalcin Allah, to me zamu ce? Allah ba marar adalci ba ne, wanda ke aiwatar da fushinsa, ko kuwa? Ina magana bisa ga tunanin mutuntaka.
6 Bazai taba zama haka ba. Domin idan haka ne ta yaya Allah zai shar'anta duniya?
7 Amma idan gaskiyar Allah ta wurin karyata ta habaka yabonsa, To me yasa ake shar'anta ni a matsayin mai zunubi?
8 To me zai hana ace kamar yadda ake fadin zancen karya a kanmu, wasu kuma sun dauka cewa mun fadi hakan, “Bari muyi mugunta, domin nagarta tazo?” Hukuncin su halal ne.
9 To me kenan? Zamu ba kanmu hujja ne? ko kadan. Domin mun riga munyi zargin yahudawa da hellinawa, da cewar dukkansu, suna karkashin zunubi.
10 Kamar yadda aka rubuta, babu wani mai adalci, babu ko daya.
11 Babu wani mai fahimta. Babu wani mai neman Allah.
12 Dukansu sun kauce hanya, dukansu gaba daya sun zama marasa amfani. Babu mai aikin nagarta, a'a, babu ko da guda daya.
13 Makogwaronsu a bude yake kamar kabari. Harsunansu na dauke da cuta. Dafin macizai na karkashin lebunansu.
14 Bakunansu cike suke da la'ana da daci.
15 Sawayensu na saurin zuwa zubar da jini.
16 Tafarkinsu wahala ce da lalacewa.
17 Wadannan mutane basu san hanyar salama ba.
18 Babu tsoron Allah a idanunsu.”
19 To mun san dai duk abin da shari'a tace, shari'a na magana ne da wadanda ke karkashinta, domin a rufe kowanne baki, domin dukan duniya ta bada amsa a gaban Allah.
20 Domin a gabansa babu wanda zai barata ta wurin ayukan shari'a. Domin ta wurin shari'a ne sanin zunubi yazo.
21 Amma yanzu ba tare da shari'a ba an bayyana sanin adalcin Allah, wanda shari'a da annabawa suke shaidawa.
22 Wato, adalcin Allah ta wurin bangaskiya cikin Yesu Almasihu ga dukkan wadanda ke bada gaskiya. Domin babu bambanci:
23 Domin duk sun yi zunubi sun kuma kasa kaiwa ga darajar Allah,
24 Da alherinsa an baratar da mu ta wurin fansar dake cikin Yesu Almasihu.
25 Amma Allah ya bayar da Yesu Almasihu wanda yake hadayar fansa ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya mika Almasihu a matsayin tabbacin hukuncinsa, sabo da kuma ketarewar zunubanmu na baya
26 cikin hakurinsa. Duk wannan ya faru ne domin a bayyana adalcinsa cikin wannan zamani, domin ya tabbatar da kansa mai hukunci, kuma ya nuna shine mai baratar da kowa saboda bangaskiya cikin Yesu.
27 To ina fahariya? An fitar da ita. A kan wane dalilin? Don ayyuka? A'a, amma ta dalilin bangaskiya.
Romawa 3 in Litafi Mai-tsarki