Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Romawa - Romawa 3

Romawa 3:5-27

Help us?
Click on verse(s) to share them!
5Amma idan rashin adalcinmu ya nuna adalcin Allah, to me zamu ce? Allah ba marar adalci ba ne, wanda ke aiwatar da fushinsa, ko kuwa? Ina magana bisa ga tunanin mutuntaka.
6Bazai taba zama haka ba. Domin idan haka ne ta yaya Allah zai shar'anta duniya?
7Amma idan gaskiyar Allah ta wurin karyata ta habaka yabonsa, To me yasa ake shar'anta ni a matsayin mai zunubi?
8To me zai hana ace kamar yadda ake fadin zancen karya a kanmu, wasu kuma sun dauka cewa mun fadi hakan, “Bari muyi mugunta, domin nagarta tazo?” Hukuncin su halal ne.
9To me kenan? Zamu ba kanmu hujja ne? ko kadan. Domin mun riga munyi zargin yahudawa da hellinawa, da cewar dukkansu, suna karkashin zunubi.
10Kamar yadda aka rubuta, babu wani mai adalci, babu ko daya.
11Babu wani mai fahimta. Babu wani mai neman Allah.
12Dukansu sun kauce hanya, dukansu gaba daya sun zama marasa amfani. Babu mai aikin nagarta, a'a, babu ko da guda daya.
13Makogwaronsu a bude yake kamar kabari. Harsunansu na dauke da cuta. Dafin macizai na karkashin lebunansu.
14Bakunansu cike suke da la'ana da daci.
15Sawayensu na saurin zuwa zubar da jini.
16Tafarkinsu wahala ce da lalacewa.
17Wadannan mutane basu san hanyar salama ba.
18Babu tsoron Allah a idanunsu.”
19To mun san dai duk abin da shari'a tace, shari'a na magana ne da wadanda ke karkashinta, domin a rufe kowanne baki, domin dukan duniya ta bada amsa a gaban Allah.
20Domin a gabansa babu wanda zai barata ta wurin ayukan shari'a. Domin ta wurin shari'a ne sanin zunubi yazo.
21Amma yanzu ba tare da shari'a ba an bayyana sanin adalcin Allah, wanda shari'a da annabawa suke shaidawa.
22Wato, adalcin Allah ta wurin bangaskiya cikin Yesu Almasihu ga dukkan wadanda ke bada gaskiya. Domin babu bambanci:
23Domin duk sun yi zunubi sun kuma kasa kaiwa ga darajar Allah,
24Da alherinsa an baratar da mu ta wurin fansar dake cikin Yesu Almasihu.
25Amma Allah ya bayar da Yesu Almasihu wanda yake hadayar fansa ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya mika Almasihu a matsayin tabbacin hukuncinsa, sabo da kuma ketarewar zunubanmu na baya
26cikin hakurinsa. Duk wannan ya faru ne domin a bayyana adalcinsa cikin wannan zamani, domin ya tabbatar da kansa mai hukunci, kuma ya nuna shine mai baratar da kowa saboda bangaskiya cikin Yesu.
27To ina fahariya? An fitar da ita. A kan wane dalilin? Don ayyuka? A'a, amma ta dalilin bangaskiya.

Read Romawa 3Romawa 3
Compare Romawa 3:5-27Romawa 3:5-27