Text copied!
Bibles in Hausa

Romawa 16:7-21 in Hausa

Help us?

Romawa 16:7-21 in Litafi Mai-tsarki

7 Ku gai da Andaranikas da Yuniyas, yan'uwana da abokan kurkukuna. Su sanannu ne cikin manzani, wadanda suke cikin Almasihu kafin ni.
8 Ku gai da Amfiliyas kaunatace na cikin Ubangiji.
9 Ku gai da Urbanas abokin aikinmu cikin Almasihu, da Istakis kaunataccena.
10 Ku gai da Abalis amintacce cikin Almasihu. Ku gai da wadanda su ke gidan Aristobulus.
11 Ku gai da Hirudiya, dan'uwa na, da wadanda ke gidan Narkissa, wadanda ke cikin Ubangiji.
12 Ku gai da Tarafina daTarafusa, masu aikin Ubangiji.
13 Ku gai da Barsisa kaunatacciya, wadda ta yi aikin Ubangiji da yawa. Ku gai da Rufas zababbe cikin Ubangiji da mamarsa da ni.
14 Ku gai da Asinkiritas da Filiguna da Hamis da Baturobas da Hamisu da kuma yan'uwa da ke tare da su.
15 Ku gai da Filolugus daYuliya da Niriyas da yan'uwansa, da Ulumfas da kuma dukan tsarkaka da ke tare su.
16 Ku gaggai da juna da tsatsarkar sumba. Dukan Ikilisiyoyin Almasihu na gaishe ku.
17 Yanzu ina rokon ku, yan'wa, ku yi tunani fa game da masu kawo rabuwa da tuntube. Sabanin koyarwar da ku ka koya. Ku yi nesa da su.
18 Domin irin mutanen nan ba sa bauta wa Ubangiji Yesu, sai dai tumbinsu. Ta dadin bakinsu suke rudin zuciyar marasa laifi.
19 Domin rayuwar biyayyarku takai ga kunnen kowa, na yi farin ciki da ku, amma ina so ku zama da hikima game da abin ya ke mai kyau, ku zama marasa laifi ga abin da ke na mugunta.
20 Allah na salama zai sa ku tattake Shaidan da sauri kalkashin sawayen ku. Alherin Ubangijin mu Yesu Almasihu ya kasance tare da ku.
21 Timoti abokin aikina, yana gaishe ku, haka Lukiyas da Yason da Susibataras da kuma yan'uwana.
Romawa 16 in Litafi Mai-tsarki