Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 9

Luka 9:6-26

Help us?
Click on verse(s) to share them!
6Daga nan sai almajiran suka tafi zuwa cikin kauyuka, suka yi ta shelar bishara, su na warkar da mutane a ko'ina.
7Ana nan Hirudus, mai mulki, ya ji labarin dukan abubuwan da su ke faruwa. Ya yi mamaki saboda wadansu mutane suna cewa Yahaya mai yin Baftisma ne ya sake dawowa da ransa.
8Wadansu kuma suna cewa, annabi Iliya ne ya sake bayyana, wadansu kuma suna cewa daya daga cikin annabawa na da can ne ya sake bayyana da rai.
9Hirudus ya ce, “Ba zai yiwu Yahaya ne ba, domin na datse masa kai. To, wanene wannan da ni ke jin wadannan abubuwa a kansa?” Daga nan sai ya cigaba da neman hanyar da zai ga Yesu.
10Sa'adda manzannin suka dawo daga tafiyarsu, suka gaya wa Yesu dukan abubuwan da suka yi. Daga nan sai ya dauke su domin su tafi tare da shi zuwa garin Baitsaida.
11Amma sa'adda taron suka ji inda Yesu ya tafi, sai suka bi shi can. Ya marabce su ya yi masu jawabi a kan mulkin Allah, kuma ya warkar da wadanda su ke bukatar warkarwa.
12Da yake yamma ta fara yi, sai almajiransa goma sha biyu suka zo suka ce da shi, “Idan ka yarda ka sallami wannan babban taron mutane dominsu shiga cikin kauyuka, da ke kewaye da gonaki, dominsu sami abinci da wuraren da za su kwana, da yake mu na nan a wurin da ba kowa.”
13Amma sai ya ce da su, “Ku ba su abin da za su ci.” Suka amsa masa, “Dukan abin da muke da shi shine, 'Yan dunkulen gurasa biyar da 'yan kifaye guda biyu, ba za mu iya zuwa mu sawo abincin da zai ishi mutanen nan su duka ba.”
14Mutanen da suke wurin sun kai kimanin mazaje dubu biyar. Sai Yesu ya ce da almajiran, “Ku ce da mutanen su zauna kungiya-kungiya, mutane hamsin a kowacce kungiya.”
15Sai almajiran suka yi haka, dukan mutanen suka zauna.
16Ya dauki dunkulen gurasan guda biyar, da kifin guda biyu, yana dubawa zuwa sama ya albakarce su, sa'annan ya gutsuttsura, ya ba almajiran domin su rarraba wa mutane.
17Dukansu suka ci kowa ya koshi. Daga nan almajiran suka tattara sauran abin da ya rage, har kwanduna goma sha biyu suka cika!
18Wata rana Yesu yana yin addu'a shi kadai, sai almajiransa suka zo sai ya tambaye su, “Wa mutane suke cewa da ni?”
19Suka amsa, “Wadansu suna cewa, Yahaya mai yin Baftisma, wadansu suna cewa kai annabi Iliya ne, har yanzu wadansu suna cewa kai wani cikin annabawa na da can ne ya dawo da rai.”
20Ya tambaye su, “Ku fa? Wa kuke cewa da ni?” Bitrus ya amsa, “Kai Almasihu ne wanda ya zo daga wurin Allah.”
21Sai Yesu ya gargade su da karfi, kada su gayawa kowa haka tukuna.
22Sa'annan ya ce, “Dan Mutum dole ya sha wahalar abubuwa da yawa; dattawa za su ki shi da manyan fristoci da marubuta, sa'annan za a kashe shi. Bayan kwana uku, za a tashe shi da rai.”
23Sai ya ce da su duka, “Dukan wanda ya ke so ya biyo ni, dole ne ya yi musun kansa, ya dauki gicciyen sa kulluyomin, ya biyo ni.
24Dukan wanda yake so ya ceci ransa, za ya rasa shi, amma dukan wanda ya ba da ransa domina, za ya cece shi.
25Wacce riba mutum zai samu idan ya sami duniya duka, amma ya rasa ransa?
26Dukan wanda yake jin kunya ta da magana ta, Dan Mutum ma zai ji kunyarsa, sa'adda ya dawo cikin darajarsa da darajar Uba da ta mala'iku masu tsarki.

Read Luka 9Luka 9
Compare Luka 9:6-26Luka 9:6-26