Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 7

Luka 7:2-8

Help us?
Click on verse(s) to share them!
2Bawan wani jarumi, wanda yake kauna, ba shi da lafiya har ma ya kusa mutuwa.
3Amma da ya ji labarin Yesu, jarumin ya aiki wadansu dattawan Yahudawa, ya ce a roki Yesu ya zo ya ceci bawansa daga mutuwa.
4Sa'adda su ka zo kusa da Yesu, su ka roke shi da gaske, cewa, “Wannan ya isa ka yi masa haka,
5saboda shi mai kaunar kasar mu ne, kuma shi ne ya gina mana majami'a.
6Sai Yesu ya tafi tare da su. Amma sa'adda ya zo kusa da gidan mutumin, jarumin ya aiki abokansa su ka ce da shi, “Ubangiji kada ka damu domin ni ban isa ka zo gida na ba.
7Shi ya sa na ga ban isa in zo wurinka ba, ka yi magana kadai bawa na kuwa zai warke.
8Gama ni ma mutum ne mai iko, ina da sojoji karkashina. Ina iya cewa da wannan, 'Ka je' sai ya tafi, in kuma ce da wani 'ka zo' sai ya zo, in kuma ce da bawa na, 'Yi kaza,' sai ya yi.”

Read Luka 7Luka 7
Compare Luka 7:2-8Luka 7:2-8