Text copied!
Bibles in Hausa

Luka 23:13-22 in Hausa

Help us?

Luka 23:13-22 in Litafi Mai-tsarki

13 Bilatus ya kira manyan firistoci tare da masu mulki da kuma taron jama'ar,
14 sai ya ce masu, “Kun kawo mani wannan mutum kamar wanda yake jagorar mutane ga munanan ayyuka, ku kuma gani, Ni, na tuhume shi a gabanku, ban sami ko kuskure daya daga mutumin nan game da abinda ku ke zarginsa da shi ba.
15 Babu, ko Hirudus ma, ya sake komar mana da shi, kun gani, babu wani abu wanda ya yi da ya cancanci mutuwa,
16 saboda haka zan yi masa horo sa'annan in sake shi.”
17 Ya zama dole Bilatus ya sakar wa Yahudawa wani daurarre guda daya lokacin idin.
18 Amma dukansu suka yi ihu tare, cewa, “A tafi da wannan mutumin, sai a sako mana Barabbas!”
19 Barabbas mutum ne wanda aka sa a cikin kurkuku saboda wani tada hankali a cikin birni da kuma kisankai.
20 Bilatus ya sake yi masu magana, yana so ya saki Yesu.
21 Amma suka yi ihu, cewa, “A giciye shi, a giciye shi.”
22 Sai ya sake ce masu sau na uku, “Don me, wace magunta wannan mutum ya yi? Ban sami wani abu da ya isa sanadin mutuwa game da shi ba. Saboda haka bayan na hore shi, zan sake shi.”
Luka 23 in Litafi Mai-tsarki