Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 9

Ayyukan Manzanni 9:5-23

Help us?
Click on verse(s) to share them!
5Shawulu ya amsa, “Wanene kai, Ubangiji?” Ubangiji ya ce, “Nine Yesu wanda kake tsanantawa;
6amma ka tashi, ka shiga cikin birnin, kuma za a gaya maka abinda lallai ne kayi.
7Mutanen da ke tafiya tare da Shawulu suka tsaya shiru sun rasa abin fada, suna sauraron muryar, amma ba su ga kowa ba.
8Shawulu ya tashi daga kasa, kuma daga ya bude idanunsa, baya ganin komai; sai suka kama hannuwansa suka yi masa jagora suka kawo shi cikin birnin Dimashku.
9Har kwana uku ba ya kallo, kuma ba ya ci balle sha.
10Akwai wani almajiri a Dimashku mai suna Hananiya; sai Ubangiji ya yi magana da shi cikin wahayi, ya ce, “Hananiya.” Sai ya ce, “Duba, gani nan Ubangiji.”
11Ubangiji ya ce masa, “Tashi, ka tafi titin da ake kira Mikakke, kuma a gidan wani mai suna Yahuza ka tambaya mutum daga Tarsus mai suna Shawulu; gama yana addu'a;
12kuma ya gani cikin wahayi mutum mai suna Hananiya na shigowa kuma ya daura masa hannu, domin idanunsa su bude.”
13Amma Hananiya ya amsa, “Ubangiji, na ji labari daga wurin mutane da yawa game da mutumin nan, da irin muguntar da ya aikata ga tsarkakan mutanenka da ke Urushalima.
14An bashi izini daga babban firist domin ya kama dukan wanda ke kira bisa sunanka.”
15Amma Ubangiji ya ce masa, “Jeka, gama shi zababben kayan aiki na ne, wanda zai yada sunana ga al'ummai da sarakuna da 'ya'yan Isra'ila;
16Domin zan nuna masa irin wahalar da zai sha sabo da sunana.”
17Sai Hananiya ya tafi, ya shiga gidan. Ya dora masa hannu a kai, ya ce, “Dan'uwa Shawulu, Ubangiji Yesu, wanda ya bayyana a gareka a hanya sa'adda kake zuwa, ya aiko ni domin ka sami ganin gari ka kuma cika da Ruhu Mai Tsarki.”
18Nan take wani abu kamar bawo ya fado daga idanun Shawulu, kuma ya sami ganin gari; ya tashi aka yi masa baftisma;
19kuma ya ci abinci sai aka karfafa shi. Ya zauna tare da almajirai a Dimashku kwanaki da yawa.
20Nan take ya fara shellar Yesu cikin haikali, yana cewa shine dan Allah.
21Dukan wadanda suka saurare shi suka yi mamaki suka ce “Ba wannan mutumin ne yake hallaka mutanen Urushalima da ke kira bisa ga wannan suna ba? Ya kuma zo nan domin ya ba da su a daure ga manyan firistoci.”
22Amma Shawulu kuwa ya sami iko sosai, kuma yana haddasa damuwa tare da rinjaya tsakanin Yahudawan dake zama a Dimashku ta wurin tabbatar da Yesu shine Almasihu.
23Bayan kwanaki da yawa, sai Yahudawan suka yi shiri domin su kashe shi.

Read Ayyukan Manzanni 9Ayyukan Manzanni 9
Compare Ayyukan Manzanni 9:5-23Ayyukan Manzanni 9:5-23