Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 8:18-33 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 8:18-33 in Litafi Mai-tsarki

18 Sa'adda Siman yaga ana bayar da Ruhu Mai Tsarki ta wurin dorawar hannuwan manzanni, ya basu kudi.
19 Ya ce, “Ku bani wannan iko, ni ma, don duk wanda na dora wa hannu ya karbi Ruhu Mai Tsarki.”
20 Amma Bitrus yace masa, “Azurfarka ta lalace tare da kai, saboda kana tunanin za ka malaki baiwar Ubangiji da kudi.
21 Baka da wani rabo a wannan al'amari, domin zuciyarka ba daidai take da Allah ba.
22 Saboda haka ka tuba daga wannan muguntarka, ka kuma yi addu'a ga Ubangiji, domin mai yiwuwa ya gafarta maka game da manufar zuciyarka.
23 Domin na gane kana cikin bacin rai da kuma cikin daurin zunubi.”
24 Siman ya amsa ya ce, “Kayi addu'a ga Ubangiji domina, kada wani daga cikin abubuwan nan da ka fada ya faru da ni.”
25 Sa'anda Bitrus da Yahaya suka bada shaida kuma suka fadi maganar Ubangiji, sun koma Urushalima; akan hanya, suka yi wa'azin bishara a kauyukan samariyawa da yawa.
26 Yanzu kuwa Mala'ikan Ubangiji ya yi wa Filibus magana cewa, “Tashi ka tafi ta kudu da hanyar da ta yi kasa daga Urushalima zuwa Gaza” (wannan hanyar yana cikin hamada.)
27 Ya kuwa tashi ya tafi. Sai ga wani mutum daga Habasha, baba ne mai babban matsayi a karkashin Kandakatu, sarauniyar Habasha. Shine yake mulkin dukan dukiyarta. Ya zo Urushalima domin ya yi ibada.
28 Yana komawa zaune cikin karussarsa, kuma yana karanta Littafin annabi Ishaya.
29 Ruhun ya ce wa Filibus, “Ka je kusa da karussar nan.”
30 Sai Filibus ya gudu ya same shi, kuma ya ji shi yana karanta littafin annabi Ishaya, sai ya ce, “Ka fahimci abin da kake karantawa?”
31 Bahabashen ya ce. “Yaya zan iya, idan ba wani ya bishe ni ba?” Ya roki Filibus ya shigo cikin karussar ya zauna tare da shi.
32 Wannan kuwa shine nassin da Bahabashen yake karantawa, “An kai shi kamar tunkiya zuwa mayanka; shiru kuma, kamar dan rago a hannun masu sosayarsa, bai bude baki ba.
33 Cikin kaskancinsa aka yi masa shari'a da rashin adalci: Wa zai bada tarihin tsararsa? Domin an dauke ransa daga duniya.”
Ayyukan Manzanni 8 in Litafi Mai-tsarki