Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 8

Ayyukan Manzanni 8:18-33

Help us?
Click on verse(s) to share them!
18Sa'adda Siman yaga ana bayar da Ruhu Mai Tsarki ta wurin dorawar hannuwan manzanni, ya basu kudi.
19Ya ce, “Ku bani wannan iko, ni ma, don duk wanda na dora wa hannu ya karbi Ruhu Mai Tsarki.”
20Amma Bitrus yace masa, “Azurfarka ta lalace tare da kai, saboda kana tunanin za ka malaki baiwar Ubangiji da kudi.
21Baka da wani rabo a wannan al'amari, domin zuciyarka ba daidai take da Allah ba.
22Saboda haka ka tuba daga wannan muguntarka, ka kuma yi addu'a ga Ubangiji, domin mai yiwuwa ya gafarta maka game da manufar zuciyarka.
23Domin na gane kana cikin bacin rai da kuma cikin daurin zunubi.”
24Siman ya amsa ya ce, “Kayi addu'a ga Ubangiji domina, kada wani daga cikin abubuwan nan da ka fada ya faru da ni.”
25Sa'anda Bitrus da Yahaya suka bada shaida kuma suka fadi maganar Ubangiji, sun koma Urushalima; akan hanya, suka yi wa'azin bishara a kauyukan samariyawa da yawa.
26Yanzu kuwa Mala'ikan Ubangiji ya yi wa Filibus magana cewa, “Tashi ka tafi ta kudu da hanyar da ta yi kasa daga Urushalima zuwa Gaza” (wannan hanyar yana cikin hamada.)
27Ya kuwa tashi ya tafi. Sai ga wani mutum daga Habasha, baba ne mai babban matsayi a karkashin Kandakatu, sarauniyar Habasha. Shine yake mulkin dukan dukiyarta. Ya zo Urushalima domin ya yi ibada.
28Yana komawa zaune cikin karussarsa, kuma yana karanta Littafin annabi Ishaya.
29Ruhun ya ce wa Filibus, “Ka je kusa da karussar nan.”
30Sai Filibus ya gudu ya same shi, kuma ya ji shi yana karanta littafin annabi Ishaya, sai ya ce, “Ka fahimci abin da kake karantawa?”
31Bahabashen ya ce. “Yaya zan iya, idan ba wani ya bishe ni ba?” Ya roki Filibus ya shigo cikin karussar ya zauna tare da shi.
32Wannan kuwa shine nassin da Bahabashen yake karantawa, “An kai shi kamar tunkiya zuwa mayanka; shiru kuma, kamar dan rago a hannun masu sosayarsa, bai bude baki ba.
33Cikin kaskancinsa aka yi masa shari'a da rashin adalci: Wa zai bada tarihin tsararsa? Domin an dauke ransa daga duniya.”

Read Ayyukan Manzanni 8Ayyukan Manzanni 8
Compare Ayyukan Manzanni 8:18-33Ayyukan Manzanni 8:18-33