Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 6:5-11 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 6:5-11 in Litafi Mai-tsarki

5 Maganar su kuwa ta farantawa dukan jama'a rai sosai. Sai suka zabi Istifanus, shi kuwa mutum ne cike da bangaskiya kuma da Ruhu Mai Tsarki da Filibus, da Birokoros, da Nikanar, da Timan, da Barminas, da kuma Nikolas, mutmin Antakiya wanda ya yi tuban Yahudanci.
6 Masu bin kuwa suka gabatar da wadannan mutanen a gaban manzannin, su kuwa suka yi masu addu'a suka kuma dora hannuwansu a kansu.
7 Sai maganar Allah ta yawaita; yawan almajiran kuwa ya rubanbanya matuka a Urushalima; firistoci da yawa na Yahudawa suka bada gaskiya.
8 Sai Istifanus, cike da alheri da iko, ya rika yin ayyukan ban mamaki da alamu a cikin jama'a.
9 Amma sai ga wadansu mutane daga wata majami'a da ake kira majami'ar Yantattu, wato su Kuramiyawa da Iskandariyawa, da kuma wasu daga kasar Kilikiya da Asiya. Wadannan mutanen kuwa suna muhawara da Istifanus.
10 Amma suka kasa yin tsayayya da Istifanus, saboda irin hikima da Ruhun da Istifanus ya ke magana da shi.
11 Sai a asirce suka zuga wasu mutane su je su ce, “Ai munji Istifanus yana maganganun sabo game da Musa da kuma Allah.”
Ayyukan Manzanni 6 in Litafi Mai-tsarki