Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 6

Ayyukan Manzanni 6:5-11

Help us?
Click on verse(s) to share them!
5Maganar su kuwa ta farantawa dukan jama'a rai sosai. Sai suka zabi Istifanus, shi kuwa mutum ne cike da bangaskiya kuma da Ruhu Mai Tsarki da Filibus, da Birokoros, da Nikanar, da Timan, da Barminas, da kuma Nikolas, mutmin Antakiya wanda ya yi tuban Yahudanci.
6Masu bin kuwa suka gabatar da wadannan mutanen a gaban manzannin, su kuwa suka yi masu addu'a suka kuma dora hannuwansu a kansu.
7Sai maganar Allah ta yawaita; yawan almajiran kuwa ya rubanbanya matuka a Urushalima; firistoci da yawa na Yahudawa suka bada gaskiya.
8Sai Istifanus, cike da alheri da iko, ya rika yin ayyukan ban mamaki da alamu a cikin jama'a.
9Amma sai ga wadansu mutane daga wata majami'a da ake kira majami'ar Yantattu, wato su Kuramiyawa da Iskandariyawa, da kuma wasu daga kasar Kilikiya da Asiya. Wadannan mutanen kuwa suna muhawara da Istifanus.
10Amma suka kasa yin tsayayya da Istifanus, saboda irin hikima da Ruhun da Istifanus ya ke magana da shi.
11Sai a asirce suka zuga wasu mutane su je su ce, “Ai munji Istifanus yana maganganun sabo game da Musa da kuma Allah.”

Read Ayyukan Manzanni 6Ayyukan Manzanni 6
Compare Ayyukan Manzanni 6:5-11Ayyukan Manzanni 6:5-11