Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 4:16-24 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 4:16-24 in Litafi Mai-tsarki

16 Suka ce, “Yaya za mu yi da wadannan mutane? Babu shakka aikin al'ajibi ya faru ta wurinsu, kuma sananne ne ga dukan mazauna Urushalima, kuma ba mu da iko mu musanci haka.
17 Amma saboda kada ya cigaba da yaduwa cikin mutane, bari mu yi masu kashedi kada su kara magana da kowa cikin wannan suna.”
18 Suka kira Bitrus da Yahaya suka dokace su kada su kara magana ko kuma koyarwa ko kadan a cikin sunan Yesu.
19 Amma Bitrus da Yahaya suka amsa suka ce, “Ko ya yi daidai a gaban Allah mu yi maku biyayya fiye da shi, ku hukunta.
20 Baza mu iya daina magana game da abubuwan da muka ji kuma muka gani ba.”
21 Bayan sun sake yi wa Bitrus da yahaya kashedi, sai suka sake su, su tafi. Domin ba su iya samu wata hujja da za su hore su a kai ba, domin dukan mutane suna yabon Allah saboda abin da ya faru.
22 Mutumin da ya sami wannan al'ajibi na warkarwa yana sama da shekara arba'in.
23 Bayan an sake su, Bitrus da Yahaya suka zo cikin mutanensu suka ba da rahoton duk abin da manyan firistoci da dattawa suka fada masu.
24 Da suka ji haka, suka daga muryarsu tare ga Allah suka ce, “Ubangiji, kai da ka yi sama da duniya da teku da duk abin da ke cikinsu,
Ayyukan Manzanni 4 in Litafi Mai-tsarki