Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 4

Ayyukan Manzanni 4:16-24

Help us?
Click on verse(s) to share them!
16Suka ce, “Yaya za mu yi da wadannan mutane? Babu shakka aikin al'ajibi ya faru ta wurinsu, kuma sananne ne ga dukan mazauna Urushalima, kuma ba mu da iko mu musanci haka.
17Amma saboda kada ya cigaba da yaduwa cikin mutane, bari mu yi masu kashedi kada su kara magana da kowa cikin wannan suna.”
18Suka kira Bitrus da Yahaya suka dokace su kada su kara magana ko kuma koyarwa ko kadan a cikin sunan Yesu.
19Amma Bitrus da Yahaya suka amsa suka ce, “Ko ya yi daidai a gaban Allah mu yi maku biyayya fiye da shi, ku hukunta.
20Baza mu iya daina magana game da abubuwan da muka ji kuma muka gani ba.”
21Bayan sun sake yi wa Bitrus da yahaya kashedi, sai suka sake su, su tafi. Domin ba su iya samu wata hujja da za su hore su a kai ba, domin dukan mutane suna yabon Allah saboda abin da ya faru.
22Mutumin da ya sami wannan al'ajibi na warkarwa yana sama da shekara arba'in.
23Bayan an sake su, Bitrus da Yahaya suka zo cikin mutanensu suka ba da rahoton duk abin da manyan firistoci da dattawa suka fada masu.
24Da suka ji haka, suka daga muryarsu tare ga Allah suka ce, “Ubangiji, kai da ka yi sama da duniya da teku da duk abin da ke cikinsu,

Read Ayyukan Manzanni 4Ayyukan Manzanni 4
Compare Ayyukan Manzanni 4:16-24Ayyukan Manzanni 4:16-24