Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 3:4-14 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 3:4-14 in Litafi Mai-tsarki

4 Bitrus da Yahaya kuwa suka zuba masa ido, Bitrus ya ce, “Ka dube mu.”
5 Gurgun nan kuwa ya dube su, yana tsammanin zai sami wani abu a wurin su.
6 Amma Bitrus ya ce, “Azurfa da Zinariya ba ni da su, amma abin da nake da shi, zan baka. A cikin sunan Yesu Almasihu Banazare, Yi tafiya”
7 Bitrus ya kama hannun damarsa, ya daga shi; nan da nan kafafunsa da kashin idon sawayensa suka samu karfi.
8 Da gurgun ya yunkura, ya mike tsaye sai ya fara takawa; ya shiga haikali tare da Bitrus da Yahaya, yana takawa, yana tsalle, yana kuma girmama Allah.
9 Dukan mutane suka gan shi yana tafiya yana kuma yabon Allah.
10 Sun lura cewa, shine mutumin da ke zama yana bara a Kyakyawar kofar haikali; sai suka cika da mamaki domin abin da ya faru.
11 Yayin da yake rike da Bitrus da Yahaya, dukan jama'a suka matso wurinsu, a gefen dakalin Sulaimanu, suna ta mamaki kwarai.
12 Da Bitrus ya ga haka ya amsa wa jama'ar, “Ya ku mutanen Isra'ila, don me ku ke mamaki?” Don me ku ka zura mana ido, kamar mu ne muka sa shi ya yi tafiya da ikon kanmu ko adalcin mu?
13 Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, Allah na iyayenmu ya girmama bawansa Yesu. Shi kuka ki kun kuma bashe shi a gaban Bilatus da ya so ya sake shi.
14 Kuka ki Mai Tsarkin nan, Mai Adalcin, maimakon haka kuka ce a sakkar maku mai kisan kai.
Ayyukan Manzanni 3 in Litafi Mai-tsarki