Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 3

Ayyukan Manzanni 3:4-14

Help us?
Click on verse(s) to share them!
4Bitrus da Yahaya kuwa suka zuba masa ido, Bitrus ya ce, “Ka dube mu.”
5Gurgun nan kuwa ya dube su, yana tsammanin zai sami wani abu a wurin su.
6Amma Bitrus ya ce, “Azurfa da Zinariya ba ni da su, amma abin da nake da shi, zan baka. A cikin sunan Yesu Almasihu Banazare, Yi tafiya”
7Bitrus ya kama hannun damarsa, ya daga shi; nan da nan kafafunsa da kashin idon sawayensa suka samu karfi.
8Da gurgun ya yunkura, ya mike tsaye sai ya fara takawa; ya shiga haikali tare da Bitrus da Yahaya, yana takawa, yana tsalle, yana kuma girmama Allah.
9Dukan mutane suka gan shi yana tafiya yana kuma yabon Allah.
10Sun lura cewa, shine mutumin da ke zama yana bara a Kyakyawar kofar haikali; sai suka cika da mamaki domin abin da ya faru.
11Yayin da yake rike da Bitrus da Yahaya, dukan jama'a suka matso wurinsu, a gefen dakalin Sulaimanu, suna ta mamaki kwarai.
12Da Bitrus ya ga haka ya amsa wa jama'ar, “Ya ku mutanen Isra'ila, don me ku ke mamaki?” Don me ku ka zura mana ido, kamar mu ne muka sa shi ya yi tafiya da ikon kanmu ko adalcin mu?
13Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, Allah na iyayenmu ya girmama bawansa Yesu. Shi kuka ki kun kuma bashe shi a gaban Bilatus da ya so ya sake shi.
14Kuka ki Mai Tsarkin nan, Mai Adalcin, maimakon haka kuka ce a sakkar maku mai kisan kai.

Read Ayyukan Manzanni 3Ayyukan Manzanni 3
Compare Ayyukan Manzanni 3:4-14Ayyukan Manzanni 3:4-14