Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 2:34-46 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 2:34-46 in Litafi Mai-tsarki

34 Dauda bai hau zuwa sama ba, amma ya ce, “Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna hannun dama na,
35 har sai na maida makiyanka abin takawar sawunka.”'
36 Saboda haka, bari gidan Isra'ila su sani tabbas wannan Yesun wanda kuka gicciye, Allah ya maishe shi Ubangiji da kuma Almasihu.
37 Da suka ji haka sai suka soku a zukatansu, suka cewa Bitrus da sauran manzanni, “'Yan'uwa me za mu yi?”
38 Sai Bitrus ya ce masu, “Ku tuba ayi wa kowannenku baftisma, cikin sunan Yesu Almasihu domin gafarar zunubanku, kuma za ku karbi baiwar Ruhu Mai Tsarki.
39 Domin alkawarin a gareku ne da 'ya'yanku da duk wadanda ke nesa, dukan iyakar mutanen da Ubangiji Allahnmu zai kira.”
40 Da maganganu da yawa ya ba da shaida kuma ya karfafa su; ya ce, “Ku ceci kan ku daga wannan muguwar tsara.”
41 Sai suka karbi maganar sa kuma aka yi ma su baftisma, a wannan rana kuma aka sami karin rayuka wajen dubu uku.
42 Su ka cigaba cikin koyarwar manzanni da zumunta, cikin kakkaryawar gurasa da kuma cikin addu'o'i.
43 Tsoro ya sauko bisa kowane rai, kuma aka yi abubuwan ban mamaki da alamu da yawa ta wurin manzannin.
44 Duka wadanda suka ba da gaskiya suna tare kuma komai nasu na kowanensu ne,
45 kuma suka saida kadarorinsu da mallakarsu kuma suka rarrabawa kowa, bisa ga irin bukatar da kowannensu yake da ita.
46 A kowace rana suka cigaba tare da nufi daya a cikin haikali, suna kakkarya gurasa a gidaje, kuma suna raba abinci tsakaninsu cikin farin ciki da tawali'u a zuciya;
Ayyukan Manzanni 2 in Litafi Mai-tsarki