Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 2

Ayyukan Manzanni 2:34-46

Help us?
Click on verse(s) to share them!
34Dauda bai hau zuwa sama ba, amma ya ce, “Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna hannun dama na,
35har sai na maida makiyanka abin takawar sawunka.”'
36Saboda haka, bari gidan Isra'ila su sani tabbas wannan Yesun wanda kuka gicciye, Allah ya maishe shi Ubangiji da kuma Almasihu.
37Da suka ji haka sai suka soku a zukatansu, suka cewa Bitrus da sauran manzanni, “'Yan'uwa me za mu yi?”
38Sai Bitrus ya ce masu, “Ku tuba ayi wa kowannenku baftisma, cikin sunan Yesu Almasihu domin gafarar zunubanku, kuma za ku karbi baiwar Ruhu Mai Tsarki.
39Domin alkawarin a gareku ne da 'ya'yanku da duk wadanda ke nesa, dukan iyakar mutanen da Ubangiji Allahnmu zai kira.”
40Da maganganu da yawa ya ba da shaida kuma ya karfafa su; ya ce, “Ku ceci kan ku daga wannan muguwar tsara.”
41Sai suka karbi maganar sa kuma aka yi ma su baftisma, a wannan rana kuma aka sami karin rayuka wajen dubu uku.
42Su ka cigaba cikin koyarwar manzanni da zumunta, cikin kakkaryawar gurasa da kuma cikin addu'o'i.
43Tsoro ya sauko bisa kowane rai, kuma aka yi abubuwan ban mamaki da alamu da yawa ta wurin manzannin.
44Duka wadanda suka ba da gaskiya suna tare kuma komai nasu na kowanensu ne,
45kuma suka saida kadarorinsu da mallakarsu kuma suka rarrabawa kowa, bisa ga irin bukatar da kowannensu yake da ita.
46A kowace rana suka cigaba tare da nufi daya a cikin haikali, suna kakkarya gurasa a gidaje, kuma suna raba abinci tsakaninsu cikin farin ciki da tawali'u a zuciya;

Read Ayyukan Manzanni 2Ayyukan Manzanni 2
Compare Ayyukan Manzanni 2:34-46Ayyukan Manzanni 2:34-46