Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 2:1-12 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 2:1-12 in Litafi Mai-tsarki

1 Da ranar Fentikos ta zo, dukansu suna tare wuri daya.
2 Nan da nan sai ga wata kara daga sama kamar ta babbar iska, kuma ta sauko ta cika duka gidan inda suke zaune.
3 Sai ga wasu harsuna kamar na wuta sun bayyana a garesu aka rarraba su, kuma suka zauna bisa kowannensu.
4 Dukansu suka cika da Ruhu Mai Tsarki suka fara magana da wadansu harsuna, yadda Ruhu ya ba su iko su yi magana.
5 A lokacin akwai Yahudawa dake zaune a Urushalima, mutanen Allah, daga kowace kasa karkashin sama.
6 Da suka ji wannan kara jama'a duk suka taru suka rude saboda kowannensu ya ji suna magana da harshensa.
7 Suka yi mamaki matuka; suka ce, “Lallai, wadannan duka ba Galiliyawa ba ne?
8 Yaya mu ke jinsu duka, kowannensu na magana a cikin harshen da aka haife mu?
9 Fisiyawa da Mediyawa da Elimawa, da Yahudawa da Kafadokiya, cikin Fontus da Asiya,
10 cikin Firgia da Bamfiliya, cikin Masar da yankunan Libiya ta wajen Sur, da baki daga Roma,
11 Yahudawa da tubabbun cikin Yahudanci, Kiretawa da Larabawa, duk munji su suna fadi a harshenmu game da manyan ayyukan Allah.”
12 Dukansu suka yi mamaki suka rikice; suka ce da junansu, “Menene ma'anar wannan?”
Ayyukan Manzanni 2 in Litafi Mai-tsarki