Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 23:5-13 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 23:5-13 in Litafi Mai-tsarki

5 Domin a rubuce yake, Ba za ku zargi shugaban mutanenku ba.”
6 Da Bulus ya ga cewa, daya bangaren Sadukiyawa ne dayan kuma Farisawa, ya yi magana da karfi a majalisa, “'Yan'uwa, ni Bafarise ne, dan Farisawa. Don tabbacin tashin matattu ne kuna shari'anta ni.”
7 Daya fadi haka, mahawara ta fara a tsakanin Farisawa da Sadukiyawa, sai taron ya rabu kashi biyu.
8 Don Sadukiyawa suka ce babu tashin matattu, babu mala'iku, babu kuma ruhohi, amma Farisawa suka ce dukan abubuwan nan sun kasance.
9 Sai mahawara ta tashi, wadansu marubutan Farisawa suka tashi da mahawara cewa, “Ba mu same mutumin nan da laifi ba sam. Ko mala'iku da ruhohi ne suka yi masa magana?”
10 Da jayayya ta tashi, babban hafsa ya ji tsoro kada su yayaga Bulus, sai ya umarce sojoji suje su kwato shi da karfi daga 'yan majalisa, su tafi da shi farfajiya.
11 Da dare Ubangiji ya tsaya kusa da shi yace, “Kada ka ji tsoro, kamar yadda ka ba da shaida game da ni a Urushalima, dole zaka sake zama shaida a Roma.”
12 Da gari ya waye, wadansu Yahudawa sun yi yarjejeniya suka dauka wa kansu la'ana: suka ce ba za su ci ba ba za su sha ba sai sun kashe Bulus.
13 Mutane fiye da arba'in suka kulla wannan makirci.
Ayyukan Manzanni 23 in Litafi Mai-tsarki