Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 23

Ayyukan Manzanni 23:5-13

Help us?
Click on verse(s) to share them!
5Domin a rubuce yake, Ba za ku zargi shugaban mutanenku ba.”
6Da Bulus ya ga cewa, daya bangaren Sadukiyawa ne dayan kuma Farisawa, ya yi magana da karfi a majalisa, “'Yan'uwa, ni Bafarise ne, dan Farisawa. Don tabbacin tashin matattu ne kuna shari'anta ni.”
7Daya fadi haka, mahawara ta fara a tsakanin Farisawa da Sadukiyawa, sai taron ya rabu kashi biyu.
8Don Sadukiyawa suka ce babu tashin matattu, babu mala'iku, babu kuma ruhohi, amma Farisawa suka ce dukan abubuwan nan sun kasance.
9Sai mahawara ta tashi, wadansu marubutan Farisawa suka tashi da mahawara cewa, “Ba mu same mutumin nan da laifi ba sam. Ko mala'iku da ruhohi ne suka yi masa magana?”
10Da jayayya ta tashi, babban hafsa ya ji tsoro kada su yayaga Bulus, sai ya umarce sojoji suje su kwato shi da karfi daga 'yan majalisa, su tafi da shi farfajiya.
11Da dare Ubangiji ya tsaya kusa da shi yace, “Kada ka ji tsoro, kamar yadda ka ba da shaida game da ni a Urushalima, dole zaka sake zama shaida a Roma.”
12Da gari ya waye, wadansu Yahudawa sun yi yarjejeniya suka dauka wa kansu la'ana: suka ce ba za su ci ba ba za su sha ba sai sun kashe Bulus.
13Mutane fiye da arba'in suka kulla wannan makirci.

Read Ayyukan Manzanni 23Ayyukan Manzanni 23
Compare Ayyukan Manzanni 23:5-13Ayyukan Manzanni 23:5-13