Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 19:9-28 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 19:9-28 in Litafi Mai-tsarki

9 Amma sa'adda wadansu Yahudawa suka taurare, suka ki yin biyayya, sai suka fara bata hanyar Almasihu a gaban taron. Saboda haka sai Bulus ya janye daga wurinsu tare da wadanda suka ba da gaskiya. Ya fara koyarwa a makarantar Tiranus.
10 Haka ya cigaba shekaru biyu har duk mazaunan Asiya suka ji maganar Ubangiji, Yahudawa da Helenawa.
11 Allah ya yi manyan al'ajibai ta hannun Bulus,
12 har marasa lafiya suka warke, mugayen ruhohi suka fito daga cikin mutane, sa'adda suka karbi kyallaye da mayafai daga jikin Bulus.
13 Amma akwai Yahudawa masu tsubu da suka biyo ta wajen, suka dauka wa kansu su yi amfani da sunan Yesu. Suka ce, “Mun dokace ku cikin sunan Yesu wanda Bulus yake wa'azinsa, ku fita.”
14 Wadanda suka yi wannan su bakwai ne 'ya'yan wani babban firist Bayahude mai suna Siba.
15 Mugun ruhun ya amsa ya ce, “Na san Yesu, na san Bulus, amma ku, su wanene?”
16 Sai mugun ruhun da ke cikin mutumin ya fada a kan matsubatan ya fi karfinsu ya kuma bubuge su. Suka runtuma da gudu suka fice daga dakin tsirara da raunuka.
17 Wannan ya zama sanannen abu ga dukan mutane, Yahudawa da Helenawa mazaunan Afisa. Suka ji tsoro kwarai, sunan Ubangiji Yesu ya sami daukaka.
18 Masu bi da yawa kuma, suka zo suka furta mugayen ayyukan da suka aikata.
19 Masu sihiri suka kawo littattafansu suka kona a gaban mutane. Da aka yi jimilar tamaninsu, aka samu sun kai dubu hamsin na azurfa.
20 Sai maganar Ubangiji ta yadu da iko ta hanyoyi da yawa.
21 Da Bulus ya kammala aikinsa na bishara a Afisa, Ruhu ya bishe shi sai ya bi ta Makidoniya da Akiya a kan hanyarsa zuwa Urushalima. Ya ce, “Bayan na je can, dole in je Roma.”
22 Bulus ya aiki almajiransa biyu Timoti da Irastus zuwa Makidoniya, wadanda suka taimake shi. Amma shi da kansa ya jira a Asiya na dan lokaci.
23 A wannan lokacin sai aka yi babban tashin hankali a Afisa game da wannan Hanyar.
24 Wani Makeri mai suna Damatrayus wanda ke kera sifoffin gunkin azurfa na Dayana, wanda sana'a ce mai kawo wa makera riba sosai.
25 Ya tattara makera ya ce da su, “Kun sa ni da wanan sana'a ne muke samun kudi mai yawa.
26 Kun gani kun kuma ji cewa, ba a Afisa kadai ba, amma har da fadin kasar Asiya wannan Bulus ya rinjayi mutane da yawa. Yana cewa babu alloli da ake kerawa da hannu.
27 Ba sana'ar mu kadai ke cikin hatsari ba, amma har da haikalin allahnmu Dayana babba zai zama mara amfani. Ta haka za ta rasa girmanta, ita da dukan kasar Asiya da duniya ke wa sujada.”
28 Da suka ji haka sai suka fusata kwarai, suka yi kira mai karfi suna cewa “Mai girma ce Dayana ta Afisa.”
Ayyukan Manzanni 19 in Litafi Mai-tsarki